Sunday

Home Hukumar 'yan sanda ta bayyana matakin da za ta dauka kan harin da aka kai jihar Kaduna
Hukumar rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, a yau Lahadi, ta sha alwashin damko wadanda suka kai hari kauyen Nandu da ke karkashin karamar hukumar Sanga ta jihar domin su fuskanci hukunci daidai da abinda suka aikata.
"Yan sanda

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai na kamfanin dillancin labarai na kasa a yau Lahadi cikin birnin Kaduna.

DSP Sabo ya bayar da shaidar cewa, hukumar 'yan sandan jihar ta gindaya jami'an tsaro sako-sako a yankunan da wannan ta'addancin ya auku inda a halin yanzu tuni sun killace gawawwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya tare da mika wadanda suka jikkata zuwa Asibiti.

Babban jami'in dan sandan ya bayyana cewa, rundunar 'yan sanda tare da hadin gwiwar dakarun sojin kasa sun bazama a yakin da wannan mummunan ibtila'i ya auku domin tabbatar da kiyaye doka da kuma kwantar da tarzoma.

Yayin tur gami da Allah wadai dangane da aukuwar wannan annoba, kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Ahmed Abdurrahman ya jajanta tare a mika sakonnin sa na gaisuwa da kuma ta'aziyya ga 'yan uwan wadanda da tsautsayin ya ritsa da su.

A cewar DSP Sabo, Kwamishinan na 'yan sandan ya gargadi al'ummar yankin Nandu da su kauracewa daukar hukuncin doka a hannayen su tare da shawartar su kan sanya idanun lura dangane da yadda hukunci na shari'a zai dauki mataki.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiya Asabar, 16 ga watan Maris na 2019, 'yan bindiga dadi suka harbe mutane 9 har Lahira tare da raunata mutane biyu gami da kone mahallan mazauna kauyen Nandu da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments