Sunday

Home Kano: Jami'an tsaro sun bawa hammata iska a cibiyar tattara sakamakon zaben gwamna
Jami'an 'yan sanda da takwarorinsu na rudunar tsaro ta farin kaya (DSS) sun bawa hammata iska a cibiyar tattara sakamkon zabe da ke hedikwatar hukumar zabe ta kasa (INEC) dake Kano.
Kano re run , sakamakon kano

An samu hargitsi a wurin karbar sakamako na INEC bayan jami'an DSS sun yanke shawarar sake tantance jama'ar da ke cikin dakin tattara sakamakon.

Jami'an DSS sun bukaci dukkan jama'ar da ke cikin dakin karbar sakamakon zaben, da suka hada da masu sa-ido da 'yan jarida da sauran su, da su fita waje domin a sake tantance su kafin barinsu su dawo cikin dakin.

Wasu jami'an DSS dauke da bindigu da aka turo daga Abuja ne suka ture 'yan sandan dake gadin bakin kofar dakin gefe guda domin gudanar da sabuwar tantance wa.
Cibiyar tattara sakamakon zabe
Hakan ne ya jawo barkewar rikici tsakanin jami'an 'yan sandan da daya daga cikin jami'an na DSS, lamarin ya kusa ya kazanta ba don wani babban jami'i ya saka baki ba.

DUBA WANNAN: Na Yi Kuskure Da Na Shiga Siyasa, Yanzu Na Tuba – Adam Zango.

Kwatankwacin irin wannan lamarin ya faru a jihar Ribasa a ranar 10 ga watan Maris, lamarin da ya tilasta INEC dakatar da dukkan harkokin tattara wa da sanar da sakamako a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewar an samu yawaitar tashin hankula a zaben kece raini da aka gudanar jiya, Asabar, lamarin da ya sa jam'iyyar PDP tayi kira da a soke zaben zaben.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments