Wasu masu yiwa kasa hidima na NYSC sun bayyana yadda wasu shugabanin jam'iyyar PDP da 'yan bangarsu suka tilasta su rubuta alkalluman karya a takardan sakamakon zabe na INEC kuma suka tilasta su rattaba hannu a kan sakamakon zaben. A yayin da ya ke tabbatar da labarin, mataimakin jami'in zabe (APO) na INEC, Michael Kponeh ya bayyana cewa 'yan daba na PDP sun tsare ma'aikatan INEC da ma'aikatan wucin gadi da bindigu a Bodo-Ogoni da ke karamar hukumar Gokana kuma suka tilasta rubuta abinda suke so.
Babban kwamandan Division 6 na Rundunar Sojin Najeriya a Fatakwal, Manjo Janar Jamil Sarham wanda ya samu wakilcin Brig Janar Adeola Kalejaiye tare da taimakon Kakakin Soji, Col. Aminu Iliyasu sunyi holen masu yiwa kasa hidima 11 tare da wasu mutane 42 da ke zargi da hannu cikin magudin zabe a jiya.
DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu - Hukumar INEC na ganawar sirri don sake duba zaben shugaban kasa
Yadda aka tilasta 'yan yiwa kasa hidima aikata magudin zabe a Rivers Source: Twitter
DUBA WANNAN : Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi Read more

Sarham ya ce: "A ranar 23 ga watan Fabrairu misalin karfe daya da rabi na rana dakarun mu da aka aike Gokana domin tabbatar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya cikin zaman lafiya sun kama mutane 39 ciki har da 'yan yiwa kasa hidima 11 da direba guda daya tare da ma'aikatan Hukumar INEC dauke da wasu muhimman kayan aikin zabe a Greenside Hotel da ke karamar hukumar Gokana. "Binciken da aka fara gudanarwa na nuna cewa an kai su Otel din ne domin suyi magudin zabe da zai baiwa wata jam'iyyar siyasa nasara. "Abubuwan da muka kwato a hannunsu sun hada da akwatunan zabe 34 dauke da kuri'un zabe, na'urorin tantance katin zabe, jakuna 10 dauke da kayan aikin zabe da mota kirar Toyota Hiace mai lamban Legas EQ 171 KRD."
Shugaban sojojin ya kuma ce an kama wasu 'yan bangan siyasa 13 a garin Harris da ke karamar hukumar Degema na jihar Rivers gabanin babban zaben na ranar Asabar.
DUBA WANNAN : Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi Read more
No comments:
Write Comments