Saturday

Home Yanzu Yanzu: Sojoji sun harbe wani barawon akwati har lahira a wata jihar Kudu
Sojojin da ke kula da tsarin gudanarwar zabe a Ukanafun sun kasha wani matashi yayinda ya tsere da akwatin zabe a mazabar kauyen Ikot Udo Ossiom, Ukanafun da ke jihar Akwa Ibom.
Lamarin wanda ya afku ne yan sa’o’i kadan ya jefa yankin cikin alhini.

Wani idon shaida ya bayyana wa majiyarmu ta The Nation cewa matashin yayi yunkurin sace akwatin zabe da safe bayan ya iso daga hukumar INEC amma sai sojojin da ke kula da mazabar suka hana shi.
Da take ci gaba da koro jawabi, Misis Elijah tace matashin ya tafi sannan ya sake dawowa mazabar domin sace akwatin a karo na biyu.
Da ya dawo a karo na biyu ne sai sojojin suka bude masa wuta inda ya mutu har lahira.

Sai dai an tattaro cewa har izuwa yanked a muke kawo rahoto gawar matashin na nan a kwance a wajen da abun ya akfku.
A baya mun ji cewa Wasu yan banga sun yadu a wasu yankunan Lokoja, babbar birnin jihar Kogi inda suke ta harbe-harbe da kwace akwatunan zabe, kamfanin dillancin labaran ta ruwaito.
A daidai lokacin wannan rahoton, mun ci cewa wasu yan banga cikin shigar yan sanda da sojoji na bogi na tsorata masu zabe a mazabun da ke kallon Bishop Delisle Catholic Cathedral a Lokoja.
No comments:
Write Comments