Monday

Home Allah da Mala'iku sun san cewa zaben fidda gwanaye na jam'iyyar APC bai gudana ba a jihar Zamfara - Marafa
Wakilin shiyyar Zamfara ta Tsakiya a zauren Majalisar dattawa, Sanata Kabiru Marafa, ya ce Allah, Mala'iku da kuma ilahirin al'umma na da cikakkiyar masaniya a zahirance cewa ba bu wani zaben fidda gwanayen takara na jam'iyyar APC da ya gudana reshen jihar Zamfara.
Marafa zamfara

Sanatan ya ce gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, ya yiwa Mahaliccin sa babban laifi na furta kalamai na rashin adalci dangane da yadda ya ke ci gaba da ikirarin zaben fidda gwanayen takara na jam'iyyar APC ya gudana a reshen jihar.

Mai Duka ya san cewa zaben fidda gwanayen takara na jam'iyyar APC bai gudana ba a jihar Zamfara - Marafa
Marafa wanda ya ke amsa tambayoyin manema labarai ya kalubalanci yadda gwamna Yari ke fafutikar neman goyon bayan shari'a a bisa rashin adalcin da ya aikata a jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara.

Ya yabawa dattako na adalci da kuma aminci na kotun daukaka kara tare da shugaban ta inda a ranar 25 ga watan Maris ta yi watsi da zaben fidda gwanayen takara da ake ikirarin gudanar sa a reshen jam'iyyar APC na jihar Zamfara.

Cikin kalami nasa, Sanata Marafa ya ce Allah Madaukakin Sarki ba ya taba barin zalunci ko rashin adalci ya yi tasiri a bisa gaskiya kuma zance na adalci sanin kowa ne ba bu wane zaben fidda gwanayen takara da ya gudana a jihar Zamfara.

KARANTA KUMA: Gubar Dalma: Yara Sama Da 150 Ke Jinya A Zamfara – MSF  

Marafa wanda ya kausasa harshe tare da bayyana takaicin sa dangane da yadda gwamna Yari ya kunyata kansa da kuma al'ummar jihar Zamfara, inda ya ke roka masa gafara da kuma afuwa ta Mai Duka sakamakon munanan ababe da ya aiwatar a jihar.

MAJIYA : LEGIT.NG
No comments:
Write Comments