Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta kausasa harshe dangane da yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ta batar da kimanin Dalar Amurka miliyan 16 wajen tanadar gidajen sauro a kasar nan.
Uwargidan shugaban kasa ta yi magana da kakkausar murya dangane da yadda gwamnatin Buhari ta batar da Dalar Amurka miliyan 16 wajen sayen gidajen sauro yayin wani taron karawa juna sani na Mata da aka gudanar cikin fadar shugaban kasa dake Abuja a ranar Asabar.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Aisha Buhari ta ce shirye-shiryen bayar da tallafi da gwamnatin tarayya ta assassa da manufa ta inganta jin dadin rayuwar al'umma, SIP (Social Investment Programmes) ba ya da wani tasiri a yankin Arewacin kasar nan.
KARANTA KUMA: Zamfara : Jerin sunayen "yan takarar Pdp da suka amfana da hukuncin kotun koli.
Cikin jawaban ta, uwargidan shugaban kasa yayin bayar da shaidar masaniyar yadda gwamnatin Buhari ta batar da dalar Amurka miliyan 16 wajen sayen gidajen sauro, ta ce kawowa yanzu babu wanda ya ribaci wannan gidajen sauro musamman a mahaifar ta ta jihar Adamawa.
Duk da mika kokon barar ta da kuma shigar da bukatar neman nata kason na gidajen sauro domin aikewa al'ummar mahaifar ta, Aisha Buhari ta ce har ila yau lamarin ya zamto tamkar an aika Bawa garin su.
SOURCE LEGIT.NG
Check this : Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki.

No comments:
Write Comments