An kwantar da mutane biyu a asibiti sakamakon rikici da ya barke tsakanin leburori Hauswa da matasan garin Idunwin-Ehigie a mahadar Egba da ke babban titin Benin zuwa Auchi.
Mutane biyun da suka samu munanan rauni sune, Osas mai gyran tayar motoci da babur da Hameed.
An kuma lalata wani masallaci da cibiyar ilimi mallakar kungiyar musulunci ta Nasrul-lahi-li Fathi Society (NAFSAT).
Matasan hausawan da rikicin ya ritsa da su sun saba zuwa mahadar Egba domin neman aikin kwadago.
Rahotanni sun bayyana cewa matasan hausawan sune zaune ne a dandalinsu a ranar Talata ne sai Osas da wasu matasa suka bukaci su tashi su bar wurin.
DUBA WANNAN: Ebola ya debo ruwan dafa kansa bayan ya sumar da budurwa a Kaduna.
Rikici ya barke tsakanin laburori Hausawa da matasan Benin, mutum biyu sun jikkata
Laburorin da ke dauke da kayayakin aikinsu kamar adda, digga, gatari da sauransu suka ki amincewa su bar wurin wanda hakan ya janyo rikici ya kaure tsakaninsu har aka yiwa Osas rauni.
Raunin da aka yiwa Osas ya fusata sauran matasan suma suka fadawa leburorin da fada su kuma masu motocci da shaguna suka rika tserewa domin su tsira da lafiyarsu.
Daga bisani matasan sun tarwatsa leburorin.
Shugaban kungiyar NASFAT reshen jihar Benin, Dr Isiaka Mustapha ya ce za a gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu cikin tayar da fitinar.
Dagajin kauyen, Pa John Aghimien ya ce karuwar leburori hausawa a unguwar yana janyo barazana ga mazauna garin.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Chidi Nwabuzor ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce an kama mutane uku da ake zargi da hannu cikin tayar da fitinar.
Ya ce yanzu hankulan al'umma ya kwanta a garin.
SOURCE LEGIT.NG

No comments:
Write Comments