Saturday

Home Duba : Jerin Jihohin Nigeria Da Akafi Fama Da Rashin Aikin Yi.
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana jerin jihohin da rashin aikin yi ya fi musu kamari a fadin Nijeriya a sulusi na uku na shekarar 2018.
Kamar yadda rahoton hukumar ya nuna a shafinta na intanet wanda Kamfanin Dillancin Labarun Nijeriya (NAN) ya yada, Jihar Akwa Ibom ita ce ta fi yawan rashin aikin yi da kashi 37.7 a cikin 100 a sulusin shekarar.
Gwamnonin Nigeria, Nigerian Governors


NBS ta kuma bayyana cewa Jihar Ribas ita ce ke biye da Akwa Ibom wajen adadin marasa aikin da kashi 36.4 a cikin 100, kana Jihar Bayelsa na biye da su da kashi 32.6 a cikin 100.
Wakazalika, a cikin jerin jihohin masu fama da rashin aikin yi bisa sikelin Hukumar Kididdigar ta Kasa, Jihar Abiya tana bin bayan Bayelsa da kashi 31.6, kana Jihar Borno mai kashi 31.4 a sulusin shekarar na uku na bara.

Rahoton hukumar ya nunar da cewa jihohi biyar da suka fi yawan adadin mutanen da ke zaman kashe wando su ne Ribas wacce take da yawan mutum milyan daya da dubu dari shida da saba’in da uku da dari tara da casa’in da daya (1,673,991), sai Akwa Ibom mai yawan milyan daya da dubu dari uku da hamsin da biyar da dari bakwai da hamsin da hudu (1,357,754), sannan Kano da take da milyan daya da dubu dari biyu da hamsin da bakwai da dari da talatin (1,257,130). Daga nan sai Jihar Legas mai yawan marasa aikin yi milyan daya da dubu tamanin da takwas da dari uku da hamsin da biyu (1,088,352), sai Kaduna da ke biye da adadin mutum dubu dari tara da arba’in da hudu da dari hudu da tamanin (940,480).

Sai dai kuma, duk da cewa Jihar Legas tana da wancan adadin na marasa aikin yi, har ila yau, NBS ta ce ita ce take da kashi mafi kankanta a cikin jerin jihohin da aka dora a sikelin kason na rashin aiki inda take da kashi 14.6 kacal.
A wani bangare na rahoton kuma, an bayyana Jihar Katsina, Jigawa, Kaduna da Yobe a matsayin jihohin da aka fi adadin aikin yi mara kwari, inda suke da kaso 39.5, 38.1, 31.0 and 30.0 duka a cikin dari.

Hukumar ta ce kason da ake da shi na adadin yawan masu aikin yi mara kwari a sulusi na uku na shekarar 2018 a Nijeriya ya kai 23.1 a cikin 100, kana adadin rashin aikin yi ya kai kashi 20.1 a cikin 100.

Rahoton hukumar ya fayyace cewa a a tsakanin sulusi na uku na shekarar 2017 zuwa na shekarar 2018, jihohi tara ne kacal suka samu nasarar rage yawan adadin masu zaman kashe wando duk da kasancewar an samu karuwar marasa aikin yi a fadin kasar nan. Jihohin da suka yi nasarar su ne: Akwa Ibom, Enugu, Imo, Kaduna, Kogi, Legas, Nasarawa, Ondo da kuma Ribas.

Hakazalika, NBS ta ce jihohi shida sun samu nasarar samar da ayyukan yi masu kwari a tsakanin sulusi na uku na shekarar 2017 zuwa na shekarar 2018, wadanda suka hada da: Legas mai adadin 740,146, sai Ribas mai adadin 235,438, Imo mai adadin 197,147, Ondo na da 142,514, Enugu kuma tana da adadin 122,333, sannan Kaduna da ta samar da adadin ayyukan yi masu kwari guda 118,929.
Kamar yadda hukumar ta yi bayani, adadin rashin aikin yi da rashin ayyuka masu kwari ya sha bamban a jihohi ne saboda yadda hada-hadarsu ta tattalin arziki suka bambanta. A cewarta, jihohin da suka fi mayar da hankali a kan aikin gona, su ne suka fi yawan samar da ayyuka marasa kwari.

Sai dai ta ce ire-iren wadannan ayyukan marasa kwari sukan iya juyawa su zama masu kwarin gaske na cikakken lokaci a lokacin damina da na girbi, saboda yadda mutane ke dukufa ga sana’ar noma na-duke-tsohon-ciniki. Kana a sauran lokutan, ayyukan wadannan manoman sai su zama marasa kwari ko kuma su bi sahun masu zaman kashe wando..

Bayan haka, wani sashe na rahoton hukumar har ila yau ya bayyana cewa jihohin da suka fi yawan adadin matan da ke zaman aure kurum a gidajensu ba su aikin komai ko kuma magidantan da ke zaman dirshan a gida ba su zuwa ko ina neman nakai, ko wadanda ba su da dabi’un kirki game da aikin yi, su ne masu karancin yawan adadin marasa aikin yi.

Dama dai ana ganin mata su ne ba su da yawan masu zaman kashe wando, tun da tun farko ba a sa su a cikin lissafin ‘yan kwadago, don haka suka yi hannun riga da aukawa cikin adadin marasa aikin yi.
Dangane da irin tsari da hanyoyin da hukumar ta yi amfani da su wurin samar da wannan kididdiga kuwa, NBS ta ce an kasafta adadin ‘Yan Nijeriya ne zuwa bangaren kwadago da kuma masu zaman dirshan a gida.

Bangaren ‘yan kwadago ya kunshi mutane masu shekara 15 zuwa 64 da haihuwa wadanda ake ganin suna da karfin da za su yi aiki, ba tare da la’akari da suna da aikin a hannu ko ba su da shi ba. A sakamakon haka, idan aka ce marasa aikin yi ana nufin mutanen da ke tsakanin shekara 15 zuwa 64 da haihuwa wadanda a tsakanin lokacin da ake wannan nazarin suna da aikin yi a hannu ko ba su da shi ko kuma suna kan nema.

Shi kuwa bangaren masu zaman dirshan a gida ya kunshi yara ne da ba su kai shekara 15 ba da haihuwa ko kuma tsofaffi wadanda suka haura shekara 64 da haihuwa ko da kuwa suna aiki don neman halaliyarsu.

SOURCE LEADERSHIP.NG
No comments:
Write Comments