Sunday

Home Yakamata Ka Saduda Hakan Nan, Cewar IBB Ga Atiku
Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya shawarci tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar babbar jam’iyyar adawa a kasar, Alhaji Atiku Abubakar, da ya saduda ya mika wuya ga sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sanar wanda ya bai wa shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, nasarar lashe shi.

IBB ya bayyana hakan ne a lokacin a sanarwar da ya bayar ta taya Shugaba Buhari murnar sake lashe zaben a karo na biyu, wanda a ka gudanar ranar 23 ga Fabrairu, 2019, ya na mai nusar da Atiku da cewa, zai janye ne ya kuma taya Buhari murna kawai don muradin kasar da kuma zaman lafiyarta, amma ba don komai ba.
Janar IBB ya kara da cewa, “Ina mai kira ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ya mance da komai ya saduda ya taya wanda ya lashe zaben murna ta hanyar da ya kamata, domin dorewar dimukradiyya a kasarmu a irin wannan lokaci mai muhimmancin gaske, amma ba don gazawarsa ba.”
Bugu da kari, Babangida ya ce, “Ina mai kira ga Atiku da ya nemi mabiyansu da su kauce wa tashin hankali da neman rigima. Dole ne su gane cewa, a tsarin dimukradiyya da zabe tilas sai an samu guda daya wanda ya yi nasara, ba don komai ba sai don hakia tsarin ya gada.”
A karshe ya yaba wa Atiku bisa tsaiwar dakarsa wajen nuna jarumta ta fuskantar takarar da ya yi tsakaninsa da shugaba mai ci, ya na mai cewa, bai yi mamakin hakan ba bisa la’akari da irin jajircewar da tsohon mataimakin shugaban kasar ya ke da ita.
Daga na sai ya yaba wa masu kada kuri’a wadanda su ka fito su ka jefa kuri’aunsu cikin mutunci da zaman lafiya ba tare da tashin-tashina ba.
A yayin da ya koma kan Shugaba Buhari, don ya taya shi murna kuwa, sai IBB ya nusar da shi cewa, bisa yadda ya lura da cewa zaben irin na kan-kan-kan ne, wanda ba a saba ganin kamarsa ba a kasar. Don haka sai ya yi kira a gare shi da ya nemo hanyoyin da za su hada kan kasar, su kuma rage damuwar da ta afku a lokacin yakin neman zaben.
“Dole ne shugaban kasar ya kauce wa kallon ’yan adawar da su ka yi takara da shi a matsayin makiya, illa ma dai ya kalle su a matsayin ’yan kishin kasa, wadanda sun saba da shi ne kawai ta hanyar yadda su ke ganin hanyoyin da za a bi a gyara kasar, don ciyar da ita gaba.

“Don haka tun da yanzu shi ne ya lashe zaben, sai ya tashi tsaye wajen sabunta kokarinsa da himmarsa wajen ganin ya tabbatar da ya fuskanci manyan matsalolin da su Najeriya ke fuskanta kamar na tsaro da fatara.
“Har yanzu Boko Haram babbar barazana ce ga kasa, musamman a yankin Arewa maso Gabas, a yain da kuma wasu manyan matsalolin guda biyu na garkuwa da mutane da fashi da makami na cigaba da zama babbar barazana a dukkan fadin kasar. Don haka dole ne shugaban kasar ya fi ba wa harkar tsaro muhimmanci,” in ji Janar Babangida.
Daga nan sai ya ja hankalin shugaban kasar kan kokarin gyara kundin tsarin mulkin kasa ta hanyar rage wani ikon da gwamnatin tarayya ke da shi zuwa wasu matakan gwamnatocin a jihohi da kananan hukumomi.
No comments:
Write Comments