Saturday

Home Tsaro: 'Yan majalisa sun bayyana sabbin hanyoyin yiwa masu garkuwa da mutane basaja
Cikin dabarun da suka bullo da ita shine dena amfani da lambar motoccinsu da ke nuna cewa su 'yan majalisun tarayya ne.
Wadanda su kayi magana da majiyar Legit.ng sun ce 'yan majalisun sun dauki wannan matakan ne saboda suna tsoron masu garkuwa da mutane.
majalissar kasa

Sun kuma ce 'yan majalisun sun dena sanar da mutane wuraren da za su tafi har hadimansu da masu aiki a gidajensu ma ba su amince da su ba a yanzu.

DUBA WANNAN: Yadda aka kama wasu daliban jami’a 2 suna zanama wani jarabawar JAMB.

'Yan majalisa sun bullo da sabuwar hanyar magance fashi da makami da satar mutane
Sun ce wasu tsirarun amintattunsu ne kadai suke sanin inda za su tafi da lokutan tafiyarsu da dawowa.

Ra'ayoyin 'yan majalisar ya rabu a kan batun tafiya tare da masu tsaron su a hirar da su kayi da Saturday Punch.

A makon da ta gabata, mun ruwaito muku cewa wasu daga cikin jiga-jigan 'yan Najeriya sun dena bin hanyar Abuja zuwa Kaduna saboda tsoron masu garkuwa da mutane.

Hakan ya sa farashin tikitin jirgin kasa ya yi tashin gauron zabi saboda yanzu al'umma sun gwammace suyi tafiya a jirgin kasan.

Wani dan majalisa daga yankin Arewa maso Tsakiya ya ce yanzu a boye ya ke tafiya inda ya kara da cewa wadanda suke tare da shi ba su sanin inda ya ke tafiya a yawancin lokuta.

Wani dan majalisar, Mr Olusegun Odebunmi ya ce baya tunanin amfani da lambar gwamnati a wajen Abuja abu ne mai kyau a yanzu saboda tsaro.

Ya ce: "Muna cikin hatsari. Idan kana zaune a cikin Abuja ne toh babu laifi idan kayi amfani da lambar gwamnati amma idan za ka fita daga Abuja zai fi kyau ka cire lambar sai dai idan kana tare da masu tsaronka na musamman."

Promote Youe business for free HERE 

No comments:
Write Comments