Kowane mutum yana so ya ga hakoransa sun kasance farare musamman mutum mai yawan murmushi. Ziyartar likitan hakori lokaci zuwa lokaci yana taimakawa mutum wajen samun hakora masu haske. Amma akwai wasu lokuta da kake so hakoran suyi karko da kuma haske saboda wani waje da zaka je. To, akwai abubuwa da zasu taimaka maka musamman a irin wannan lokacin.
Na Biyu 2 : Ta hanyar Amfani da kayan kanti (stores)
A takaice
Zamu bayani akan wadannan abubuwan
- Amfani da injin laser.
- Aje wajen likitan goge hakori.
- Amfani da Whitening strip.
- Amfani da man goge hakori mai saka haske.
- Amfani da whitening pen.
- Amfani da hydrogen peroxide.
- Amfani da baking Soda.
- A guji cin abincin da zai dafar da hakori.
- Aci strawberry.
Na Daya 1 : Ta hanyar Amfani da kayan Asibiti.
- Yin Amfani da injin laser. - Wannan injin yana aiki sosai matuka amma kumafa yana da tsada sosai, Za’a shafa man goge hakori a jikin hakoran sannan a sanya robar a saman hakori. Daga nan kuma sai a haska laser din. Yana daukar kamar a mintuna 30 anayi. duba hoton kasa.
- Zuwa wajen likitan goge hakora. - Yana da matukar amfani kamar duk bayan wata shida aje wajen likita domin wankin hakora, hakan yakan taimaka wajen kare hakoranku daga duk wani abu mara kyau, mai cutarwa.
- Yin Amfani da Whitening strip - Ana siyar dashi a kantina da stores, Yadda ake amfani da shi shine anso ayi amfani da guda biyu kawai a rana daya, idan anje wajen saya a duba ciki idan akwai -chlorine dioxide- to kar a saya don yana lalata dadashin hakori a kula sosai, Bayan an tabbatar da ingancinsa sai a bude a lika guda 1 a hakoran sama, dayan kuma a hakoran kasa sai a barsu kamar minti 30 a jiki, zaku iya cigaba da amafani da shi kamar tsawon sati 2 don samu kyakkyawan sakamako.
- Yin Amfani da man goge hakori - Shi man goge hakori bashi da saurin fitar da dattin hakori idan aka kwatanta shi da sauran hanyoyi , amma yana taimakawa wajen tsaftace hakora da kuma sawa baki kamshi.
- Yin Amfani da whitening pen - Shi kuma wannan yanayinsa kamar biro na rubutu yake, Amma akwai mai na hasken hakori a ciki, Yadda ake amfani da shi, idan aka bude sai a dan murda kan don fito da man, sai a tsaya a gaban madubi a bude baki yadda za'a iya ganin hakora, sai ayi amfani da biron ayiwa hakoran fenti, bayan an gama sai a bar bakin a bude kamar 30second , Amma kar aci ko a sha wani abu sai kamar bayan mintuna 45, Za'a iya cigaba da yi a sau daya a rana har tsawon kwana 30 don samun sakamako mai kyau.
whitening pen
Na Uku 3 : Yin AAmfani da Abubuwan Gida.
- Yin Amfani da hydrogen peroxide - Wannan yana taimakawa sosai wajen haskaka hokori, bashida wata illa sosai matukar dai ba hidiya akayi ba, Yadda ake amfani da shi , a samu tsaftataccen tsumma sai a tsoma aciki ruwan ma sai a goge hakoran ko kuma a kuskure baki da murfi daya na ruwan, ko kuma a tsoma brush na wanke baki a cikin man sai a goge hakora da brush din, a kula sosai kar a hadiya.
- Yin Amfani da baking Soda - Itama baking soda tana taimakawa wajen haskaka hakoran mutum a cikin kankanin likaci Yadda ake amfani da shi , A samu tsumma ko tawul tsaftatacce a goge hakora, sai a jika brush na goge baki da ruwa sai a tsoma cikin bakin soda sai a goge baki kamar yadda aka saba yi kullum, ayi hakan kamar na tsawon minti uku, a kula da kyau ita bakin soda ta na lalata dadashin hakora kon haka kar ace za'a dinga amfani da ita akullum, za'a iya amafani da ita sau biyu kawai a cikin mako guda.
- A guji cin abinci da zai iya dafar da hakori - Idan ana bukatar hakora su zauna fes-fes da haskensu , to ya kasance an guji yawa shan ko cin abubuwa masu dafar da hakori, kamar irinsu bakin shayi, coffee, da sauransu. Idan kuma kana yawan amfani da irin wadannan abin sha to za'a iya cin cingum marar sugar bayan an kammala shan abin ko kuma ya kasan ce kana amfani da abin zuka, ko kuma ka shafa vaseline kadan a kan hakoran kafin ka fara shan irin wadannan abubuwa masu dafar da hakori.
- Aci strawberry - Bayan angama abinci, a samu strawberry aci tana matukar taimakawa wajen tsaftace hakora, idan ba'a samu strawberry ba za'a iya amfani da Apple , karas ko pear suma suna da amfani wajen tsaftace hakora bayan anci abinci.
No comments:
Write Comments