Wednesday

Home Babban Dalilin da yasa sarki sunusi II bai halarci rantsuwar Ganduje ba.
Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya noke ya ki halartar taron rantsar da gwamnan jahar Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje a karo na biyu daya gudana a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito duk da tsare tsaren da gwamnatin tayi na jera yadda Sarkin tare da sabbin sarakunan jahar masu daraja ta daya zasu zauna, amma Sarkin bai halarta ba, duk da cewa kujerarsa ce ke dauke da lamba 1.

KU KARANTA: Kotu ta kara kwace kujerar majalisar wakilai daga hannun APC, ta umarci INEC ta bawa PDP.  

Sai dai ana rashin halartarsa taron baya rasa nasaba da rikicin dake tsakaninsa da gwamnatin jahar Kano, tun bayan da Gwamna Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu da zasu yi gogayya dashi, wanda hakan ke alanta kokarin Ganduje na rage masa izza.

Amma rahotanni sun tabbatar da cewa duka sabbin sarakunan da suka hada da Sarkin Rano, Sarkin Bichi, Sarkin Gaya da Sarkin Karaye duk sun halarci taron rantsarwar ta Ganduje a matsayin gwamnan Kano karo na biyu.

Da misalin karfe 10:30 na safe ne Alkalin Alkalan jahar Kano ya rantsar da Ganduje da mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna a gaban dubun dubatan magoya baya da yayan jam’iyyar APC da suka halarci taron daya gudana a filin wasa na Sani Abacha.

A yayin da yake gabatar da jawabinsa, Gwamna Ganduje ya sanar da bada ilimi kyauta ga duk wasu masu fama da nakasa yan asalin jahar Kano tun daga matakin Firamari har zuwa matakin gaba da sakandari.

SOURCE LEGIT.NG

No comments:
Write Comments