Friday

Home Hotuna : Shugaba buhari yayin sallar jumu'a Yau A Saudiyya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi sallar Juma'a a babban masallacin Makkah da ke Saudiyya tare da kimanin shugabanin kasashen duniya 53 da daruruwan mabiya addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa Buhari da sauran shugabanin kasahen duniya sun tafi kasa mai tsarkin ne domin hallartar taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) karo na 14.

Taron wadda Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud ne mai masaukin baki zai fara ne misalin karfe 12 na dare.

Wadanda suka yiwa shugaba Buhari rakiya sun hada da gwamnonin jihar Osun, Niger da JIgawa.

An sa ran shugaba Buhari zai gana da wasu shugabani kasashen duniya kafin ya dawo gida Najeriya a ranar Lahadi kamar yadda NAN ta ruwaito.


Shugaba Buhari da shugaban NITDA, Aliyu Pantami da Shugaba Macky Sall na Senegal a Makkah


Shugaba Buhari tare da takwararsa na kasar Chadi, Idris Deby bayan sallar Juma'a a Makkah


Shugaba Buhari tare da shugaban kasar Chadi, Idris Deby bayan sallar Juma'a a masallacin Makkah

DUBA WANNAN: Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba


Shugaba Buhari da Shugaba Idris Deby na Chadi da Macky Sall na Senegal bayan sallar Juma'a a Makkah

SOURCE LEGIT.NG

No comments:
Write Comments