Lamarin sace mutane da yin garkuwa da su ya shigo masana’antar shirin fim din Hausa ta Kannywood, inda a jiya Laraba a ka sace shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan fim fa kasa, Malam Salisu Muazu a kan hanyarsu ta koma wa garin Jos daga Kaduna.
Yayansa Malam Sani Muazu ne ya sanar, inda ya bayyana cewa, “jiya a kan hanyarmu ta komawa Jos daga Kaduna bayan halartar wani taro, mu ka yi kicibis da ‘yan fashi/masu satar mutane a guraren Saya bayan Jengere a yankin karamar hukumar Bassa da ke jihar Filato.
DUNA WANNAN : Kannywood: Kotu ta janye dokar kama wata shahararriyar yar fim din Hausa da ta bayar a baya.
Alhaji Sani, wanda kuma tsohon shugaban MOPPAN ne na kasa, ya kara da cewa, sun samu tuntubar da su a safiyar yau Jumaa, inda a ka nemi a biya diyyar Naira miliyan 10.
Daga nan sai ya roki a sanya su a addu’a tare da fatan Allah ya kawo karshen matsalar tsaron nan a fadin kasar bakidaya.
SOURCE LEADERSHIP. NG

“Sun yi ma na fashi, amma na yi sa’a na tsira, sai dai kuma kanina, Salisu Muazu da wasu abokai guda biyu da mu ka rage wa hanya zuwa Jos a kan hanyarsu ta zuwa Bauchi, Danlami Yanke-yanke da Bature, wadannan Fulanin maharan su sun sace su.”
Alhaji Sani, wanda kuma tsohon shugaban MOPPAN ne na kasa, ya kara da cewa, sun samu tuntubar da su a safiyar yau Jumaa, inda a ka nemi a biya diyyar Naira miliyan 10.
“Sun tuntube mu a safiyar nan, su na masu neman a biya diyyar Naira miliyan 10, in ji shi.
Daga nan sai ya roki a sanya su a addu’a tare da fatan Allah ya kawo karshen matsalar tsaron nan a fadin kasar bakidaya.
SOURCE LEADERSHIP. NG
No comments:
Write Comments