Saturday

Home Mun shirya tsaf don tunkarar zaben gwamnoni , cewar Prof. Mahmood Yakub.
Jiya Juma’a Shugban Hukumar zabe ta kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da cewar, Hukumar ta shirya tsaf don gudanar da zabukan da za a gudanar a ranar Asabar. 9 ga watan Maris, 2019, a jihohi 29 da ke fadin kasar nan.
Farfesa Mahmood ya bayyan hakan ne a ganawar da Hukumar ta shirya da Kwamishinonin Hukumar.

An dai gudanar da ganawar ce bayan da Hukumar ta sanar da sunan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaman zakakaran da ya lashe zaben kujerar shugaban kasa a karkashin inuwar jami’yyar APC tare da kuma kammala zabukan ‘yan majalisar dattawa da na wakilai ranar Asabar da ta gabata.

A cewar Farfesa Yakubu an gudanar da ganawar ce don yin nazari da sauransu a kan zabukan da aka gudanar ranar Asabar da ta wuce domin yin wasu gyare-gyaren da suka dace.

Ya sanar da cewar, ganawar za ta taimaka yadda Hukumar za ta tinkari zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokn jihohi da ke tafe.

KARANTA WANNAN : Malamin addinin da ya yi hasashen faduwar Buhari Amma yanzu ya sake magana.

A cewarsa, tun fil azal, da ma idan Hukumar ta gudanar da zabuka takan yi nazari a kan zabukan da nufi magance matsalolin da Hukumar ta fuskanta a baya kafin gudanar da wasu zabuka.
A karshe Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce, tuni sun yi nisa a kan gudanar da shirye-shiryen zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki da ke tafe.
No comments:
Write Comments