Showing posts with label hotuna. Show all posts
Showing posts with label hotuna. Show all posts

Friday

Hotuna : Shugaba buhari yayin sallar jumu'a Yau A Saudiyya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi sallar Juma'a a babban masallacin Makkah da ke Saudiyya tare da kimanin shugabanin kasashen duniya 53 da daruruwan mabiya addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa Buhari da sauran shugabanin kasahen duniya sun tafi kasa mai tsarkin ne domin hallartar taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) karo na 14.

Taron wadda Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud ne mai masaukin baki zai fara ne misalin karfe 12 na dare.

Wadanda suka yiwa shugaba Buhari rakiya sun hada da gwamnonin jihar Osun, Niger da JIgawa.

An sa ran shugaba Buhari zai gana da wasu shugabani kasashen duniya kafin ya dawo gida Najeriya a ranar Lahadi kamar yadda NAN ta ruwaito.


Shugaba Buhari da shugaban NITDA, Aliyu Pantami da Shugaba Macky Sall na Senegal a Makkah


Shugaba Buhari tare da takwararsa na kasar Chadi, Idris Deby bayan sallar Juma'a a Makkah


Shugaba Buhari tare da shugaban kasar Chadi, Idris Deby bayan sallar Juma'a a masallacin Makkah

DUBA WANNAN: Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba


Shugaba Buhari da Shugaba Idris Deby na Chadi da Macky Sall na Senegal bayan sallar Juma'a a Makkah

SOURCE LEGIT.NG

Thursday

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya sauka a birnin Madina : Hotuna

Mun samu cewa a Yammacin yau Alhamis, 16 ga watan Mayun 2019.

shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Madina na kasar Saudiya domin gudanar da ibadar Umarah a cikin wannan babban wata na Azumin Ramalana.

DUBA WANNAN : Kwana Casa'in - Kashi Na Shida 6 - AREWA24.  

Buhari in makka

Ziyarar shugaban kasa Buhari ta yi daidai da amsa goron gayyata na masarautar Saudiya karkashin jagorancin Sarki Salman Bin Abdulaziz kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana.






Saturday

Bidiyo : Gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje Yayin Tabbatar da Nadin sarakunan Yanka.

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR da Mataimakin sa Dr Nasiru Yusuf Gawuna sum iiso dakin taro na Sani Abacha Stadium domin bikin karbar takardun sababbin Sarakunan Rano, Bichi, Karaye da Gaya wanda aka basu jiya Jumu'a.

ganduje
Sarakunan hudu da aka yiwa nadin sun hada da; Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila, Sarkin Gaya Alhaj Ibrahim Abdulqadir Gaya, Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Karaye Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II.

KARANTA WANNAN : Dalilan da yasa kotu ta yi gaggawar dakatar da Ganduje   

Yayin bikin nadin sarautan, Gwamna Ganduje ya ce sabbin masarautun da aka kirkira za su inganta masarautar Kano.
"Mun san cewa wannan sabbin masarautun za su inganta tsaro da ilimi," a cewar Ganduje.

Gwamnan ya kuma ce gwamnati za ta sanar da ranakun da za a yiwa sarakunan bikin nadi na musamman a nan gaba.

alumma

A baya dai kunji cewar kotu a kano ta dakatar da  gwamnati kan batun nadin sabbin sarakunan, sai dai lokacin da labarin dakatar da gwamnatin jihar Kano da kotu tayi daga kafa sabbin masarautu a jihar Kano, kwamishinan shari’ah na jihar, Barista Ibrahim Mukhtari ya bayyana cewa har zuwa daren ranar Juma’a, 10 ga watan Mayu, bai amshi wani umurni daga kotu akan lamarin nadin sabbin saranan ba.



READ HERE: Top 5 animal that has the longest life span.  



The vedio from Arewasound-channel.

 Da farko dai an rawaito cewa wata babbar kotun jihar Kano, ta dakatar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga kafa sabbin masarautu hudu da majalisar dokokin jihar ta yi.


Monday

Yanzu-Yanzu : Abba Kabir Yusuf ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi (Hotuna)

A ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu, dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben da aka kammala, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), ya kai wa babban shehun darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ziyara a gidansa dake Kano.
Abba kabar yusuf, abba gida gida, abba gida gida song, wakar abba gida gida

Dan takarar ya samu rakiyar dan takarar mataimakinsa, Kwamred Aminu Abdulsalam, tare da wasu magoya baya da masoyan sa.

Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi
Abba kabar yusuf, abba gida gida, abba gida gida song, wakar abba gida gida


Abba Gida-Gida a gidan Dahiru Dahiru Bauchi

Jam’iyyar tana nema kotu ta soke nasarar da gwamna mai-ci Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC mai mulki ya samu a zaben na bana.

DUBA WANNAN: Kannywood : Hotunan Adam A. Zango da sabuwar amaryar sa 

PDP tana so ne a ba ‘dan takararta, Injiniya Abba K. Yusuf nasara a zaben na 2019. Lauyoyin PDP sun fadawa kotun karar zaben cewa ‘dan takarar ta na 2019, Abba Kabiru Yusuf, ya samu kuri’un da ake nema wajen lashe zaben gwamna don haka ta nemi a bayyana shi a matsayin zababben gwamna na jihar Kano.
Abba kabar yusuf, abba gida gida, abba gida gida song, wakar abba gida gida

Abba Gida-Gida a gidan Dahiru Dahiru Bauchi.
Abba kabar yusuf, abba gida gida, abba gida gida song, wakar abba gida gida

Abba Gida-Gida ya ziyarci Dahiru Bauchi
Abba kabar yusuf, abba gida gida, abba gida gida song, wakar abba gida gida

A karar da PDP ta maka a gaban kotun mai sauraron korafin zabe mai shafi 1685. Jam’iyyar hamayyar tana ja da soke zaben wasu yankuna a cikin karamar hukumar Nasarawa da hukumar zabe mai zaman kan-ta tayi a watan jiya.

Sunday

Kannywood : Hotunan Adam A. Zango da sabuwar amaryar sa

Zango ya angonce da wata mai suna Safiya Umar Chalawa, wacce aka fi kira da Suffy, a ranar juma'a, 26 ga watan Afrilu, da misalin karfe 2:30 na rana.
Adam a zango da amaryarsa,  amaryar adam a zango

An daura auren ne a masallacin fadar sarkin Gwandu da ke garin Gwandu, a jihar Kebbi.

Majiyar mu ta sanar da mu cewar Zango ya yi aure sau biyar a baya, ya samu 'ya'ya shida; hudu maza, biyu mata, daga mata biyar da ya aura kafin su rabu.
Adam a zango da amaryarsa,  amaryar adam a zango

Sabuwar amaryar Zango
Adam A. Zango da sabuwar amaryar sa
Adam A. Zango da amaryar sa

DUBA WANNAN: Dandalin Kannywood: Dalilan da suka sa zan kai Hadiza Gabon kara kotu - Amina Amal

Amina ce matar Zango ta farko da ya aura a shekarar 2006. Ita ce uwar yaron sa na farko, Haidar, wanda yanzu haka ya cika shekara 12 da haihuwa. Majiyar mu ta ce ba ta san abinda ya raba auren Zango da Amina ba.

Zango ya kara auren wata matar mai suna A'isha, 'yar asalin Shika ta karamar hukumar Zaria a jihar Kaduna. Ta haifa masa 'ya'ya maza uku.
Adam a zango da amaryarsa,  amaryar adam a zango

Jarumin ya auri matar sa ta uku mai suna Maryam daga jihar Nasarawa.

Daga bisani ya auri wata jarumar fim mai suna Maryam AB Yola a Lugbe, Abuja a shekarar 2013. Sun bayyana tare a cikin wani shirin fim din Hausa mai suna 'Nas'.

DUBA WANNAN: Mutane 5 Masu HAtsari a Duniya Da Ake Nemansu Ruwa a Jallo  

A shekarar 2015, Zango ya auri Ummul Kulsum daga Ngaoundere a jamhuriyar Kamaru. An yi auren a sirrance. Ummul Kulsum ce ta fara haifa wa Zango diya mace, wacce ya sanya wa suna Murjanatu.

Safiyya ko kuma Suffy kamar yadda ake kiranta, ita ce za ta kasance matar Zango ta shida da ya aura.
Majiyar mu ta ce Zango ya saki dukkan mata biyar da ya aura a baya, sai dai har yanzu ba ta san dalilin rabuwar sa da matan da ya ke aura ba.

Monday

Hotuna : Shugaban Sojin sama ya nishadantar da Sojoji dake yaki da Boko Haram

Babban hafsan rundunar mayakan Sojan sama, Air Marshal Saddique Abubakar ya shirya ma zaratan dakarun Sojin saman Najeriya dake fafatawa a filin daga na jahar Borno, liyafar cin abinci tare da nishadantar dasu.

Sadiqque ya shirya wannan liyafar ce a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu a garin Maidugurin jahar Borno, inda aka ci abinci mai rai da lafiya tare da nama iya nama, aka kuma sha kayan shaye shaye da tande tande, sa’annan aka nishadantu da dadadan wakokin bare bari.

KU KARANTA: Kwana Casa'in Kashi Na 3 : AREWA24 Channel.   

Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Sojan sama, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda yace Saddique na amfani da damar irin wannan liyafa don ganawa da dakarun Sojinsa a duk lokacin da ake wani sha’anin biki, don haka ya shirya musu wannan saboda bikin Easter da kiristoci ke yi.

Kaakakin ya kara da cewa Saddique na amfani da wannan dama don gode ma Sojojinsa, tare da jinjina musu bisa kokarin da suke yi wajen yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas, sa’annan yace irin wanna taro na dauke ma Sojojin kewar rashin iyalansu a kusa.

Babban hafsan Sojan sama ya nishadantar da Sojojin dake yaki da Boko Haram
Haka zalika baya ga Sojojin da suka halarci liyafar, rundunar ta gayyaci al’umma unguwar Gomari, unguwar da sansanon rundunar Sojan sama take zuwa wannan liyafa, inda kuma dayawansu suka amsa kira, suka ci, suka sha, suka yi nak!.

Daga karshe kaakaki Daramola yace rundunar ta gudanar da irin wannan liyafar cin abinci a sansaninta dake Yola, da kuma sansaninta dake jahar Katsina.

SOURCE LEGIT.NG

Friday

Hotuna : A karon farko Anyi Nasarar Daukar Hoton Ramin Zurmiya Na Duniya (Black Hole)

Masu binciken sararin samaniya sunyi nasarar daukar hoton ramin zurmiya na black hole....
A karon farko, masana binciken sararin samaniya sunyi nasarar daukra hoton ramin zurmina na duniya, abinda ake kira black hole a turance. Shi da ramin black hole shine ginshikin duk duniyoyi da ake iya gani a sararin samaniya kamar yadda bincike ya nuna.
fisrt black hole, black hole na farko

Masanan sunyi amfanin da na’urar Event Horizon Telescope (EHT), wadda ke amfani da jeri-jerin maduban hangen nesa, wato telescopes, da aka giggirka su a kusurwowi daban daban na duniya don leqen abubuwan dake wakana a sararin samaniya.
Hoton ramin, an dauke shi ne a ma’unin M87, wanda yazo daidai da tafiyar shekaru miliyan 55 a kirgar duniyar taurari.

“Wannan hoton da kake gani, yana nuna mana inda ba wani mahaluki da ya taba gani kafin yau” inji Dr Heino Falcke, wani jami’n biciken sararin samaniya na EHT, a lokacin ganawa da maneman labarai, yau a Brussels. Ya kara da cewa “Ni a ganina na, tamkar ace mun dan leko kofar wuta ne”.

DUBA WANNAN : Lauyoyi 12 Ne Za Su Nemawa Amina Amal Hakkinta. 


HOTUNA 


First black hole

First black hole

First black hole

First black hole

Dan zobe-zoben dake kewaye da hoton wannan rami dai yazo daidai da hasashen da masanin kimiyyar makamashi, wato Albert Eeinstein ya yi don kwatanta karfin maganadison dake riqe da duniya, wato gravity.


Wannan hoto dai shine sheda mafi inganci dake tabbatar da samuwar ramin zurmiya na black hole da nau’rar Event Horizon ta hasko.





Saturday

HOTUNA : Buhari ya gana da Sarki Abdullahi Husseini II na Jordan.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Sarkin Jordan, Sarki Abdullahi bin Al-Hussein II a bayan fagen taron tattalin arziki na yankin Gabas Ta Tsakiya da Afirka Ta Yamma da aka gabatar a birnin Amman na kasar Jordan.

Buhari in jordan


Buhari ya mika godiyarsa ga Sarki Abdullahi bisa irin gudunmawar da ya ke bawa Najeriya wurin yaki da ta'addanci da ta ke yi.
president buhari in jordan

Top3


Mai taimakawa shugaban kasa a fanin watsa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar a Abuja inda ya bayyana cewa shugaba Buhari ya yabawa Sarki Abdullah II.

DUBA WANNAN: An kori diyar 'dan majalisar tarayya da aka gano tana aiki da takardun bogi

Shugaba Muhammadu Buhari da tawagarsa tare da Sarki Abdullahi Hussain II na kasar Jordan

Shugaba Buhari ya ce goyon bayan da kasashen duniya ke bawa Najeriya, musamman kasar Jordan ya nuna cewa kasashen na duniya sun shirya hada kansu wuri daya domin zaman tsintsiya madaurinki daya wanda hakan zai haifar da zaman lafiya mai dorewa.

buhari in jordan


Shugaba Muhammadu Buhari tare da Sarki Abdullahi Hussein na kasar Jordan
Muhammadu Buhari zai bar Birnin Amman da ke kasar Jordan ne gobe Lahadi 7 ga Watan Afrilun 2019. Daga nan ne ake sa ran shugaban kasar na Najeriya zai gana da manyan kasar UAE a wani zama na musamman da za ayi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin ganarwarsa da Sarkin kasar Jordan, Abdullahi Hussaini II

Kamar yadda labari ya zo mana dazu nan, Mai Martaba Sarkin Dubai kuma Firayim Minista na kasar UAE, Sheikh Mohammed Bin Rachid Al Maktoum, shi ne ya gayyaci shugaba Buhari zuwa taron da aka shirya a cikin kasar sa.

Za a yi wannan zama ne da manyan shugabannin Duniya game da harkar bunkasa tattalin arzikin kasashe ta hanyar shigowar hannun jari. Wannan zama da za ayi yana cikin manyan taron da aka saba gani na kasashen Duniya.

READ MORE : Buhari ya gana da Sarki Abdullahi Husseini II na kasar Jordan (Hotuna) Read more: https://hausa.legit.ng/1231878-buhari-ya-gana-da-sarki-abdullahi-husseini-ii-na-kasar-jordan-hotuna.html

Thursday

Hotuna : Yadda gwamna elrufai ya fatattaki masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja


Wani jawabin da mai magana da yawun gwamna, Samuel Aruwan, ya saki ya nuna cewa a jiya Laraba, gwamnan ya nufi birnin tarayya Abuja sai ya isa kauyen Akilubu misalin karfe 3:40 na rana, kawai sai ya hagi tarun motoci kan hanya inda sukace masu garkuwa da mutane na kan gaba.

KU KARANTA: A karon farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano.

Yace: "Jami'an tsaron gwamnan sun kawar da masu garkuwa da mutanen wadanda suka arce cikin daji."
"Bayan bude hanyar, gwamna El-Rufa'i ya bada umurnin cewa wadanda yan bindigan suka jiwa rauni a kaisu asibiti da gaggawa."
"Kana gwamnan ya umurci jami'an tsaro su tsananta sintiri a hanyar domin kawar da yan barandan."

GA HOTUNAN




DUBA KUMA
Top3




You may Like the vedio? WATCH IT HERE

Sunday

Zafafan Hotunan Fatima Ganduje bayan shekara guda da auren ta. : HOTUNA

A halin yanzu shekara guda kenan bayan da Fatima Abdullahi Ganduje, diyar gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, da ta auri Idris Ajimbi, 'da ga gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi. An yi shagali na kece raini yayin bikin su a brinin Kano da kuma Oyo.
fatima ganduje wedding ,fatima ganduje
fatima ganduje wedding, fatima ganduje
Ko shakka ba bu tarihi ya tabbatar da cewa, anyi shagulgula na bugawa a jarida yayin bikin auren su a birnin Ibadan da kuma Kano inda ya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance Waliyyin Amarya da ya karba ma ta sadaki na N50,000 yayin daurin aure a fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
fatima ganduje wedding, fatima ganduje
fatima ganduje wedding, fatima ganduje
Jiga-jiga da dama a fadin kasar nan sun halarci shagalin bikin 'ya'yan Gwamnonin biyu inda aka yi itifakin yadda kimanin Gwamnoni 20 suka halarta baya ga Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, Ministoci, 'Yan Majalisar tarayya da kuma hamshakan Attajirai.

DUBA WANNAN : Yanzu-Yanzu - Hukumar INEC na ganawar sirri don sake duba zaben shugaban kasa 
fatima ganduje wedding. fatima ganduje
fatima ganduje wedding, fatima ganduje
Jaridar Legit.ng ta ruwaito, an shafe tsawon kwanaki ana buduri inda bayan shekara guda a jiya Asabar, Amarya Fatima ta watsa wasu zafafan hotunan ta tare da Sahibinta a shafin ta na zauren sada zumunta tare da mika godiya ga Mai Duka da ya yi mata wannan babban arziki da Albarka. 
fatima ganduje wedding, fatima ganduje

fatima ganduje wedding, fatima ganduje

Saturday

Hotuna : Yanzu Yanzu obasanjo ya kada kuri'arsa.


Rahoton da muke samu yanzu na nuni da cewa tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Aremu Obasanjo ya kada kuri'arsa a mazabarsa da ke ward 11 unit 22 a harabar gidan Olusomi da ke Abeokuta a karamar hukumar Abeokuta ta Arewa.

An dai fara kada kuri'a a mazabar ne tun sa'o'i uku da suka gabata a yawancin mazabu da ke jihar ta Abeokuta.

A hirar da ya yi da manema labarai gabanin jefa kuri'arsa, Obasanjo ya yi kira ga al'umma su fito kwansu da kwarkwata su jefa kuri'arsu domin zaban shugabanin da za su jagorance su.

Sunday

HOTUNA : SHUGABA BUHARI YAYIN CIN ABINCI DA SHUWAGABANNIN KASASHEN DUNIYA A FARANSA.

Shugaba Buhari ya samu damar ganawa da babban sakataren majalisar dinkin duniya (MDD), Antonio Guterres, da ragowar shugabannin kasashe da dama domin tattauna yadda za a hada karfi da karfe domin samun zaman lafiya a kowanne bangare na duniya. A daren jiya, Asabar, ne jaridar Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Faransa domin halartar taron kasa da kasa a kan zaman lafiya da za a yi, a karo na farko, tsakanin ranakun 11 da 13 ga watan Disamba, 2018. Read more: https://hausa.legit.ng/1203276-buhari-ya-ci-abinci-tare-da-shugabannnin-duniya-a-kasar-faransa-hotuna.html
Shugaba Buhari ya samu damar ganawa da babban sakataren majalisar dinkin duniya (MDD), Antonio Guterres, da ragowar shugabannin kasashe da dama domin tattauna yadda za a hada karfi da karfe domin samun zaman lafiya a kowanne bangare na duniya. A daren jiya, Asabar, ne jaridar Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Faransa domin halartar taron kasa da kasa a kan zaman lafiya da za a yi, a karo na farko, tsakanin ranakun 11 da 13 ga watan Disamba, 2018. Read more: https://hausa.legit.ng/1203276-buhari-ya-ci-abinci-tare-da-shugabannnin-duniya-a-kasar-faransa-hotuna.html
Shugaba Buhari ya samu damar ganawa da
babban sakataren majalisar dinkin duniya
(MDD), Antonio Guterres, da ragowar
shugabannin kasashe da dama domin tattauna
yadda za a hada karfi da karfe domin samun
zaman lafiya a kowanne bangare na duniya.

A daren jiya, Asabar, ne jaridar Legit.ng ta rawaito labarin cewar shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya isa kasar Faransa domin
halartar taron kasa da kasa a kan zaman lafiya
da za a yi, a karo na farko, tsakanin ranakun 11
da 13 ga watan Disamba, 2018.

Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna
Shugaba Buhari ya samu damar ganawa da babban sakataren majalisar dinkin duniya (MDD), Antonio Guterres, da ragowar shugabannin kasashe da dama domin tattauna yadda za a hada karfi da karfe domin samun zaman lafiya a kowanne bangare na duniya. A daren jiya, Asabar, ne jaridar Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Faransa domin halartar taron kasa da kasa a kan zaman lafiya da za a yi, a karo na farko, tsakanin ranakun 11 da 13 ga watan Disamba, 2018. Read more: https://hausa.legit.ng/1203276-buhari-ya-ci-abinci-tare-da-shugabannnin-duniya-a-kasar-faransa-hotuna.html

Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna
Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna

Kafin ya dawo Abuja, shugaba Buhari zai gana
tare da tattaunawa da 'yan Najeriya mazauna
kasar ta Faransa.
Daga cikin 'yan rakiyar shugaba Buhari akwai;
gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina,
gwamna Willie Obiano na jihar Anambra, da
gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti. Ragowar
'yan rakiyar su ne; ministan harkokin waje,
Geoffrey Onyeama; ministan shari'a, Abubakar
Malami; mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Babagana Monguno; da babban darektan hukumar leken asiri ta kasa, Ahmed Abubakar.

Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna

Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna

Wednesday

Hukumar Zabe Ta Kasa Ta Fitar Da Jadawalin Zabuka Na 2019 : Nigeria

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta shirya zabukan shugaban kasa da na majalissun kasa na 2019 a ranar Asabar, 16 ga Fabrairu, yayin da za a gudanar da zabukan gwamnoni dana "yan majalissun jahohi ranar Asabar, 2 ga watan Maris na shekarar 2019. Kamar yadda kuke gsni a hoton kasa.

SOURCE@INEC

Saturday

HOTUNA : "Yan Sanda Sun Damke "yan Bangar Siyasa A Kano.

A yau Juma’a ne rundunar ta 'yan sanda reshen jihar Kano ta yi gabatarwa manema labarai wasu 'yan bangar siyasa wadanda aka kama a yayin zabubbukan fidda gwani na jam’iyyu daga Talata 2 zuwa Juma’a 5 ga watan Oktoban 2018.


 Cikin wadanda aka kama har da wani dan fashi da makami wanda an dade ana nemansa wato Bashir Musa da aka fi sani da Gachi wanda ke addabar Unguwannin Hotoro, Na'ibawa, Mariri da sauransu a birnin Kano. 


Kakakin rundunar yansandan jihar Kano, SP Magaji Musa Majia ya ce sun kama 'yan bangar siyasar da mugayen makamai masu yawa da suka hada da adda, barandami, sanduna da wukake. Yace dukkanin yandaban da ke hannun su zasu mika su zuwa kotu domin ayi musu hukunci dai dai da abinda suka aikata. 


Daga karshe SP Majia, ya tabbatar da cewa rundunarsu za ta cigaba da aiki ba dare ba rana wajen kame duk wasu 'yan bangar siyasa a Jihar Kano don ganin anyi zaben shekara ta 2019 cikin lafiya da kwanciyar hankali.