Wani rahoto da jaridar Guardian ta wallafa ya nuna wakilinta ya yi kundunbalar sanin halin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke ciki a gidan da yake a London, wanda ya sa ‘yan sanda suka yi awon da gaba da ‘dan jaridar.
Wannan lamari ya jawo karin kira ga ‘yan Najeriya da su fahimci tsarin doka da shugaban ya rubutawa Majalisa tafiyarsa da mika mulki ga mataimakinsa Yemi Osinbajo.
A labarin da dan jaridar ya rubuta dake lissafa motoci da yawan mutanen da ke shiga masaukin na shugaban Najeriya, ya ce bai nemi izinin zuwa gidan ko magana da wani daga ofishin jakadanci ba, amma ya nace sai wani da bashi da hurumi yayi magana da shi a ma’aikatan gidan.
Yayin da kakakin shugaba Buhari Femi Adesina, yake karin bayani kan halin da shugaban ke ciki, ya ce babu wani abin tayar da hankali kan lafiyar shugaban.
Ya kara da cewa mutane ne suka zabi shugaban don haka a rika mutunta abubuwan da yake fada.
No comments:
Write Comments