Karya ka ke yi, ba za mu mutu ba: PDP ta maidawa Obasanjo raddi
Jam’iyyar PDP mai adawa na ta fama da rikice-rikice tun bayan zaben 2015. Har ta kai tsohon shugaban kasa Obasanjo yace PDP ta mutu ta lalace. Jam’iyyar ba ta kyale sa haka ba.
Bangaren Ahmed Makarfi na Jam’iyyar PDP ya maidawa tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo raddi bayan kalaman sa da yake cewa Jam’iyyar PDP ta mutu ta lalace. Obasanjo yace tun bayan da ya bar mulki Jam’iyyar ta fara tan gal-tan gal.
Walid Jibrin wanda shi ne shugaban kwamitin BOT yace Obasanjo ya rufewa mutane baki. Alhaji Jibrin yace za a kawo rikicin PDP ba tare da Obasanjo ya sa baki ba kamar yadda ya fice ya bar Jam’iyyar.
Jam’iyyar tace tana yi wa tsohon shugaban fatan alheri amma ba ta ga dalilin ya rika tsoma baki bayan ya bar Jam’iyyar ba. Kawo yanzu dai abubuwa sai kara tabarbarewa suke yi a Jam’iyyar ta PDP mai adawa.
Shugaban Jam’iyyar ta PDP Ali Modu Sheriff yace babu dalilin da zai sa ya sauka daga kujerar sa sannan kuma ya sha alwashin hana kafa wata sabuwar Jam’iyya karkashin PDP din. Da alamu dai bangaren su Sanata Makarfi suna shirin kafa wata sabuwar Jam’iyya mai suna APDP.
No comments:
Write Comments