Rahotanni daga Lardin jihar Arewa mai nisa ta 'kasar Kamaru. na cewa.
Jagorar mata mabiya akidar Shi'a ta jagoranci wata 'karamar tawaga mai 'kunshe da mata kimanin 7 ciki hada sakatariyar 'kungiyar inda suka yi taron manema labarai suka kuma bayyana cewa sun fita daga shi'a.
"Hajjiya Balkissou Mammane" ita ce shugabar matan a Lardin Arewa mai nisa kuma ta umarci sakatariyar 'kungiya mai suna "Murjannatou Soulyeman" da-ta karanto sanarwar a gaban manema labarai tare da sauran wadanda suka fita daga shi'ar.
KU KARANTA :- Shugaba Buhari ya kafa tarihin a yau, ku karanta dalilai 3
Sai dai sakatariyar ta bayyana cewa ba dawowar da shugaban Najeriya "Muhammadu Buhari" ya yi ce tasa suka fita daga shi'a ba a'a kawai sun fuskanci cewa uwar kungiyar a Najeriya ba-ta mutunta muradunsu shi yasa suka yanke shawarar ficewa daga 'kungiyar inda ta 'kara da cewa za su gudanar da addinin Musulunci babu ruwansu da bin wata akida.
No comments:
Write Comments