Shugaba Muhammadu Buhari ya maida martanin rade-raden masu yimar fatan mutuwa a kwanaki da suka gabata da dawowarshi a yau, Juma'a, 10 ga watan Maris.
Yayin da Shugaba Buhari yake yin jinya a garin Landan dake kasar Birtaniya, an bayar rahoto cewa mijin Aisha Buhari ya mutu. Amma, fadar shugaban kasa ta saki hotuna daban daban da suka musanta jita-jitar mutuwarshi.
KU KARANTA: Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya
A safiyar yau, Juma'a, 10 ga watan Maris ne Shugaba Buhari ya dawo kasa nan. Jirgin samarshi ta sauko a filin jirgin samar Kaduna.
Kafin yau, shugaban Najeriya ya karbi bakunci manyan yan siyasa a gidan shugaban Najeriya dake garin Landan. Kuma ya kira wasu shugabannin duniya da yana nan da rai, bai mutu ba.
A lokacin da ya bar kasar a watan Janairun bana na hutunshi, wasu yan Najeriya suka jin tsoro bisa lafiyarshi. Kuma, wasu yan jam'iyyar adawa musamman gwamnan jihar Ekiti ya fada cewa Shugaba Buhari bashi da karfi da lafiya zai jagorantar Najeriya.
A ra'ayoyin wasu yan Najeriya, shugaban kasan yayi abubuwa ban mamaki a yau domin ya dawo.
No comments:
Write Comments