A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar Birtaniya inda yaje aka duba lafiyansa bayan kwashe kwanaki 50 a can.
Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya.
Duk dayake al’umma da dama na farin ciki da dawowar shugaba Buhari, kuma zaka gane haka daga shafukan yanar gizo inda jama’a da dama ke bayyana farin cikinsu da yi ma shugaban fatan alheri, yayin da da kuma wasu ke zuba ruwa a kasa suna sha, wasu kuma ke hada taron gangamin nuna farin ciki a garuruwa daban daban.
Sai dai duk da haka akwai wasu kason yan Najeriya da ko kadan basa farin ciki da dawowar shugaba Muhammadu Buhari gida Najeriya.
A Cikinsu akwai:
KU KARANTA: Yanzun nan: Buhari ya umarci Osinbajo ya cigaba rikon kwarya, yana bukatan hutawa kadan
1. Jam’iyyar adawa
Tun bayan tafiyar shugaba Buhari ne dai jam’iyyar PDP ta fara caccakar gwamnatinsa da shi kansa, inda har daga cikinsu suka dinga kiraye kirayen da yayi murabus, wasu kuma suka dinga yada jita jitan wai ya mutu. Don haka dawowarsa cikin koshin lafiya yayi matukar razana su.
2. IPOB
Rukunin ýan Najeriya 5 da basa murnar dawowa shugaba Buhari gida Najeriya
Kungiyar nan mai karajin samar da kasar Biafra, IPOB wanda a yanzu haka shugaban su Nnamdi Kanu ke kame a hannun gwamnati inda yake fuskantar shari’a zasu yi matukar bakin cikin dawowan shugaba Buhari, musamman yadda ya dawo cikin koshin lafiya.
3. "Yan Shia’a
Da shugaba Buhari ya fara dadewa a kasar Birtaniya bayan tafiyansa, sai yan shi’a suka fara watsa labaran karya wai cewa ai tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mutu, inda wasu daga cikinsu suke rantsewa da Allah cewa lallai Buhari ya mutu, har ma an samu wata mata da tace muddin Buhari ya dawo ta bar addinin Shi’a. toh yanzu da Buhari ya dawo bamu san halin da zasu shiga ba.
4. MASSOB
Haka zalika suma kungiyar MASSOB dake da manufa iri daya da IPOB na fafutukan samar da kasar Biafra zasu yi bakin ciki da dawowar shugaba Buhari Najeriya, saboda sun nuna ba’a tare da shugaban tun da fari.
5. Barayin gwamnati
Yaki da cin hanci da rashawa da shugaba Buhari yake yi a kasar ta girgiza barayin gwamnati da dama a kasar nan, don haka dayawa daga cikin ire iren barayin nan ba zasu taba yin fatan Buhari ya dawo gida Najeriya ba.
No comments:
Write Comments