Saturday

Home Anyi kira ga "Yan Arewa dake kudu dasu garzaya subar yankin.

An nemi ‘Yan Arewa mazauna Yankin su bar
Kudancin kasar zuwa gobe. A sakon da ya fito
tun kwanaki an ba ‘Yan Arewa wa’adi zuwa
wannan wata. Haka dai kwanaki wasu ‘Yan
Arewa su ka kira ‘Yan kudu su bar masu
kasa.

Mun samu wani sako da ake barazana da
‘Yan Arewa mazauna Kudancin Najeriya. A
sakon dai da ba a san daga inda ya fito ba an
nemi ‘Yan Arewa su tattara ina su-ina su su
bar kasar kafin gobe wanda ita ce Ranar
farko na watan Yuli.

biafara, yan arewa, kudu, kabilanci, tarzoma, kasar kudu, kasar arewa, arewacin nigeria



A Sakon da aka fitar an yi kira ga Mazauna
Yankin da kakkasusar murya su bar Kasar
Kudu ko kuma su ga abin da zai faru da su.


A sakon mai maganar yace yana da makaman
da zai yaki Hukuma babu kakkautawa.
Mun samu labari cewa kwanaki 27 ga Watan
nan ne Gwamna Nyesom C Wike na Jihar
Ribas ya kai ziyara har fadar Sultan watau
Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad III tare da
tawagar sa ta Sarakunan gargajiya a Jihar
Sokoto inda yace ba ya goyon bayan a raba
Najeriya.

– Ana dai ta irin wadannan yunkuri a halin
yanzu a kasar.

Source NAIJ HAUSA
No comments:
Write Comments