- Sanatocin kasar nan sun ce fasa kaurin da ake
yi a Najeriya yayi yawa matuka
- Kwamitin Majalisar tace kayan da ake shigo da
su a sace sun wuce na Tiriliyan 7
Shugaban kwamitin da ke kula da harkar
shigo da kaya cikin Najeriya a Majalisar
Dattawa Sanata Hope Uzodinma ya koka da
yadda ake shigo da kaya ta barauniyar hanya
cikin kasar.
Majalisar tace Bankin Duniya ya bayyana
cewa kayan da ake fasa kaurin su a Najeriya
sun haura Tiriliyan 7 a kowace shekara
wanda ya zarce kasafin kudin kasar. Bukola
Saraki yace idan har ana so ayi matsalar
tattalin arzikin dole a shawo kan wannan
matsala.
Saraki ya bayyana babban matsalar Gwamnatin APC
Shugaban Majalisar Dattawan kasar nan
Bukola Saraki yace muddin Hamid Ali yayi
maganin harkar fasa-kauri a Najeriya to ya
sa duk tufafin da ya ga dama ko wandon
turoza ne da 'yar fikikiyar riga ko ma wane
iri. Saraki yace shi zai ma mara masa baya a
kan wannan kudiri.
Daga :Naij.com Hausa
No comments:
Write Comments