Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba daidai ba ne kalaman da mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi cewa gwamnatinsa ta karbi N4.5tr, yana mai cewa N1.5tr ta karba.
A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar ya ce, "Ina matukar mutunta mai martaba saboda shi sarkina ne; domin ni dan Kano ne. Amma akwai gyara a alkaluman da ya bayar.
Gaskiya ne gwamnati ta karbi kudi sosai daga babban bankin Najeriya, amma ba ta zarta ka'ida ba."
Shi dai Sarki Muhammadu Sanusi ya ce kudin da gwamnati ta karba daga babban bankin Najeriya sun ninka sau fiye da goma kan adadin da doka ta ba su umarni.
Sai dai Malam Garba Shehu ya kara da cewa, "Mu dauka maganar da ya fada gaskiya ce. Duk da haka gwamnati tana da kudin da ya zarta wanda ta karba a ajiye a asusun bai-daya. Kamar mutum ne mai asusun banki biyu; daya babu kudi, dayan akwai makudan kudi. Menene illar kwaso kudin daya asusun domin biyan bukatar al'umma?."
Kakakin na shugaban Najeriya ya ce ba zai yi wa Sarki Sanusi raddi kan adawar da yake yi ga kudirin gwamnati na karbi bashin $30bn, yana mai cewa ministar kudi za ta tanka masa.
A cewarsa, "A matsayi na na dan kasa zan so na sake karanta jawabinsa game da wannan batu. Amma ai za a karbo bashin ne domin yin ayyukan ci gaban kasar, cikinsu har da kafa layukan jirgin kasa da samar da hasken wutar lantarki."
(Source=bbchausa)
No comments:
Write Comments