
Al’amarin ya afku ne a garin Agege dake
jihar inda mutane da dama suka rasa
rayukansu.
Hatsarin dai ya faru ne ta sanadiyar kauce hanya da jirgin yayi daga kan kwangiri a
safiyar yau Alhamis, 16 ga watan Nuwamba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar,
Olarinde Famous-Cole ya tabbatar da
afkuwar al’amarin, in da ya kara da cewa,
jirgin ya kuma ci karo da wata katuwar
motar daukan kaya.
Famous-cole ya ce, a yanzu haka, an tura
jami’an tsaro wurin da hatsarin ya faru
amma bai bada alkaluman mutanen da suka
mutu ba.
Ba a karon farko kenan ba da ake samun
hatsarin jirgin kasa a garin Agege mai cike da
hada-hadar jama’a.
No comments:
Write Comments