Tuesday

Home 2019: Buhari yayi wa Majalisar Dinkin Duniya alkawarin tabbatar da gaskiya da adalci a zabe mai zuwa
Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da Majalisar Dinkin Duniya cewar yayi alkawarin tabbatar da gaskiya, da adalci a zaben mai zuwa na shekarar 2019.
Shugaban yayi bayanin hakan a lokacin da Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta gana dashi a Abuja; A wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniyar ta bayar daga birnin New York. "A shirye - shiryen zaben da ake yi na shekarar 2019, da kuma irin goyon bayan da Majalisar Dinkin Duniya take nuna akan hakan, Shugaba Muhammadu Buhari yayi maraba da irin kokarin da Majalisar Dinkin Duniyar ta ke yi. Sannan kuma ya tabbatar da Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar cewar yayi alkawarin tabbatar da gaskiya da adalci a zaben da za ayi." Amina Mohammed ta ziyarci Najeriya a ranar 23 zuwa ranar 25 ga wannan watan, a yayinda ta gana da Shugaba Buhari tare da manyan jami'an gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki a Abuja. 2019: Buhari yayi wa Majalisar Dinkin Duniya alkawarin tabbatar da gaskiya da adalci a zabe mai zuwa Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da Majalisar Dinkin Duniya cewar yayi alkawarin tabbatar da gaskiya, da adalci a zaben mai zuwa na shekarar 2019. Shugaban yayi bayanin hakan a lokacin da Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta gana dashi a Abuja; A wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniyar ta bayar daga birnin New York. "A shirye - shiryen zaben da ake yi na shekarar 2019, da kuma irin goyon bayan da Majalisar Dinkin Duniya take nuna akan hakan, Shugaba Muhammadu Buhari yayi maraba da irin kokarin da Majalisar Dinkin Duniyar ta ke yi. Sannan kuma ya tabbatar da Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar cewar yayi alkawarin tabbatar da gaskiya da adalci a zaben da za ayi." Amina Mohammed ta ziyarci Najeriya a ranar 23 zuwa ranar 25 ga wannan watan, a yayinda ta gana da Shugaba Buhari tare da manyan jami'an gwamnati da kuma masu ruwa da tsaki a Abuja. Majalisar Dinkin Duniyar ta ce shugaban kasar da Mataimakiyar Sakatare Janar din sun tattauna manyan batutuwa guda hudu: Babban Zabe na shekarar 2019, fitar da masu neman mafaka 'yan kasar Kamaru, yarjejeniyar cinikayya ta Afirka, da kuma matsalolin tsaro a yankin arewa maso gabas. "A halin da ake ciki yanzu akan 'yan gudun hijirar kasar ta Kamaru da suke shigowa Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakiyar Sakatare Janar sun amince akan subi dokar da duniya ta gindaya game da hakkokin 'yan gudun hijira da masu neman mafaka musamman ma na kasar Kamaru. "A bangaren yarjejeniyar kasuwanci na yankin Afrika kuwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da Mataimakiyar Sakatare Janar din cewar Najeriya tana da shirin shiga tsarin amma har sai bayan yayi shawarwari da al'ummar kasa. "Game da matsalar tsaro kuwa a yankin Arewa maso Gabs na kasar nan, Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakiyar Sakatare Janar din sun nuna jin dadin su game da dawo da 'yan matan da 'yan ta'addar Boko Haram suka yi. SUn kuma bukaci hukumomin tsaro da su mai da hankali wurin tabbatar da tsaro a makarantu musamman ma na yankin da abin ya shafa." Ranar Lahadi dinnan ne Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ta bar Najeriya.
SOURCE @HAUSA.NAIJA.NG
No comments:
Write Comments