Wanda bai ji bari ba, tabbasa zai ji hoho, inji malam bahaushe, kwatankwacin lamarin da ya faru kenan a jihar Kaduna, inda wani mutumi mai suna Ewuga da yayi dare dare a saman falwaya ya fado ya mutu. Wannan lamari ya faru ne a ranar Takata 27 ga watan Maris, a unguwar bayan Loco dake garin Kafanchan a karamar hukumar Jema’a na jihar Kaduna, inda Ewuga ya hau kan falwaya da nufin mayar da wayoyin wutar da kamfanin wuta suka yanke masa, sakamakon rashin biyan kudin wuta.
Daily Trust ta ruwaito Ewuga, wanda ma’aikacin wucin gadi ne da hukumar lantarkin ta KAEDCO, yayi nasarar mayar da wayoyin wutar, amma sai zuma suka taso masa, inda a garin ya kauce ma zumar ne, sai ya tabo wayar wutar, nan take ya mutu. ma’aikacin NEPA Majiyar NAIJ.com ta ji ta bakin wani dan unguwar, wanda yace: “A kokarinsa na kauce ma zumar ne ya taba wata wayar wuta, nan take ya fadi matacce tun kafin a kai masa agaji”
SOURCE @↓↓
https://hausa.naija.ng/1160490-aiki-ya-kwana-wani-maaikacin-nepa-ya-gamu-da-ajalinsa-a-saman-falwaya.html#1160490
Thursday
Home ›
labarai
labaran abin Al'ajabi
›
Wanda bai ji bari ba, tabbasa zai ji hoho, inji malam bahaushe,
WELCOME TO AREWASOUND
VISIT OUR NEW BLOG
- - Latest Hausa song
- - Newest Android games
- - Useful Android Apps
- - Hausa Novels
- - Health Tips
- - How to make money online 2019
AREWASOUND.COM>>> Is Your Best Solution.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Write Comments