Saturday

Home A kashe duk wanda Aka gani da makami : cewar gwamnan zamfara AbdulAziz yãri.
Gwamnan ya ce, bisa la'akari da irin abubuwan da ke faruwa a wasu kauyuka na jihar, gwamnatinsa ta zauna tare da jami'an tsaro da sauran mahukunta inda aka dauki mataki don ganin irin haka ba ta sake faruwa ba.
Abdul'aziz Yari, ya ce, matakin da aka dauka shi ne, gwamnatin jihar ta bayar da umarnin cewa duk wanda aka kama na rike da bindigar da ake aika-aika da ita, idan soja ko dan sanda ya gan shi, to ba bukatar a bar shi ya sake kwana a doron kasa. Saboda a cewar gwamnan, wanda aka kaman shi ma ya kashe mutane ba adadi, don haka zamansa a cikin al'umma masifa ne. Ya ce, an dauki wannan mataki ne bisa la'akari da umarnin Allah (SWT), don haka babu wani da-na-sani a kan wannan mataki. Kazalika gwamnan ya ce, daga yanzu duk wanda aka kama yana taimaka wa irin wadannan mutane da ke kashe jama'a a jihar da wanda ke karbar kudi kamar na fansa ya kai musu idan sun yi garkuwa da mutane duk hukunci iri daya za a yi musu. Gwamnan ya ce ba bu wani zancen zuwa kotu idan an kama irin wadannan mutanen, hukunci kawai za a dauka a kansu na kashe su ba tare da bata lokaci ba.
No comments:
Write Comments