Saturday

Home Hotuna: Rahama Indimi, surukar IBB ta saki kyawawan hotunan da suka rikita dandallin sadarwar zamani
Diyar hamshakin mai kudin nan na Najeriya sannan kuma surukar tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja watau Ibrahim Badamasi dake zamar tsohuwar matar dan sa Muhammed Babangida mai suna Rahama Indimi ta saki zafafan hotunan ta sa dandalin sada zumunta.


Rahama Indimi mai kimanin shekaru 41 a duniya dai a hotunan ta caba adon maida tsohuwa yarinya domin tabbas duk wanda ya ganta zai ce shekarun ta ba su kai hakan ba.

NAIJ.com ta samu dai cewa a shekarar 2016 ne dai Rahama Indimi din ta rabu da mijin na ta bayan sun shafe shekaru akalla 14 a tare tare da samun zuri'a a tsakanin su.


<

Haka ma dai mai karatu zai iya tuna cewa daya daga cikin 'ya'yan hamshakin mai kudin yanzu haka yana auren diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, watau Zahra Buhari.
No comments:
Write Comments