Yan sandan kasar Indiya sun kama wani dan shekaru 43 a garin Kolkata daya ajiye gawar mahaifiyarsa a cikin firinji har na tsawon shekaru uku yana amfani da zanen yatsar hannunta yana karban fanshon ta. Asirin sa ya tonu ne yayinda Yan sanda suka gano gawarta a gidansa ranar Alhamis.
A yayinda yake zantawa da jaridar Indian Express, mataimakin kwamishinan yan sanda Nilanjan Biswas yace, "An ajiye gawar Bina Mazumdar ne a cikin firinji tun shekarar 2015. Muna cigaba da binciken dalilin da yasa aka ajiye gawar ta."
Yan sandan sun kuma ce wanda ake zargin, Subhabrato Mazumbar yana tsare kuma za'a cigaba da bincike kafin a gurfanar dashi. Wata majiya daga yan sandan ta bayyanawa cewa mahaifiyar mai shekaru 87 da rasu ne a dalilin buguwar zuciya. Kafin rasuwarta, Bina ma'aikaciyar gwamnati ce a hukumar Abinci na indiya amma daga baya tayi murabus. Bayan rasuwar ta Subhabrato ya cigaba da karban fansho Rs 50,000 a kowane wata kuma mahaifinsa yana da masaniya kan lamarin. Subhabrato dalibi ne mai karantar fasahar jima da kuma yana sayar da fata. Yan sanda sun gano takardan shedar cewa Bina tana raye amma na bogi ne. Daga baya ma bincike ya nuna cewa Subhabrato yana da tabin hankali.
Read more:

No comments:
Write Comments