Monday

Home Kashe 'Yan Shi'a : Hukumar NRHC Tace Za Tayi Bincike.
Hukumar ta NHRC ta tabbatar da cewa za ta
duba zargin da ke kan Rundunar Sojojin Najeriya
da kuma Jami’an ‘Yan Sandan kasar na kashe
Mabiya addinin Shi’a babu gaira babu dalili da
aka yi daga shekarar 2014 zuwa 2018 a cikin
Najeriya.



NRHC ta tabbatar da hakan ne a wata wasika da
ta aikawa babban Lauyan nan da ke kare hakkin
Bil Adama watau Femi Falana. Falana ya aikawa
Hukumar takarda kwanaki inda ya nemi ta
binciki yadda Gwamnati ke tauyewa jama’a
hakkin su.

Femi Falana SAN ya zargi Gwamnatin Tarayya da Buhari yake jagoranta da amfani da Jami’an
tsaro wajen yi wa ‘Yan Shi’a kisan mummuke
tare da hana su magana da yin addinin su da
kuma fita tattaki da yin dandazo kamar yadda su ka saba.

Falana ya bayyana cewa an kashe Mabiya
addinin Shi’a fiye da 492 a cikin shekaru 4
musamman a cikin Garin Zaria, Kaduna, Sokoto,
Kano, da kuma Birnin Tarayya Abuja bayan
daure Jagoran Kungiyar IMN Ibrahim Zakzaky da aka yi tun 2015.

Kwanan nan tsohon Gwamna Ayodele Peter
Fayose ya soki Gwamnatin Buhari game da kashe 'Yan Shi'a a Kasar da aka yi a cikin Garin Abuja.
Fayose yace bai dace a harbi ‘Yan Shi’a da ke
fito-na-fito da Sojoji ba.

SOURCE@LEGITHAUSA
No comments:
Write Comments