Sunday

Home Zaben 2019: Dalilin da ya sa muka watsawa Atiku kasa a idanu - ACF
Kungiyar ACF yayin ganawa da manema labarai kan ababe da suka shafi kasar nan a halin yanzu, ta bayyana dalilin da ya sanya ta juya wa Atiku Abubakar baya, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a babban zabe na ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata.
Atiku sad

Babban sakataren kungiyar, Anthony Sani, ba ya ga yabawa ingataccen zabe da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ta gudanar a fadin kasar nan, ya kuma fayyace dalilai da suka sanya kungiyar ACF ta yi watsi da Atiku a zaben bana.

Duk da cewa ba ya daga cikin tsare-tsare da kuma akidun kungiyar ACF ta mara baya ga kowane dan takara, Mista Sani ya ce kungiyar ta yi watsi da Atiku a sakamakon kudirin sa na sauya fasalin kasa da kuma mallaka wasu bangarorin gwamnati a hannun 'yan kasuwa.

A yayin da an kamanta wannan kudiri na sauya fasali a lokutan baya musamman a siyasance da kuma tattalin arziki ba tare da haihuwar wani 'da mai ido ba, kungiyar ACF ta ce kudirin Atiku na sauya fasalin kasar nan ba zai yi wani tasiri ba fidda ita zuwa tudun tsira.

Kazalika kungiyar ACF ta ce kudirin Atiku na sauya fasalin kasar nan da kuma manufar sa ta sayar da kamfanin man fetur kasa watau NNPC, shi ne babban dalilin da ya sanya ta marawa shugaban kasa Buhari baya a zaben bana da kuma duba ya zuwa kwazon gwamnatin sa.

KARANTA KUMA: Zaben kano : - Yanzu haka ana cigaba da tattara sakamakon zaben | ku biyomu ta nan.

Sakataren ACF ya ce kungiyar ba ta da wani haufi dangane da yadda babban zabe na bana ya gudana, illa iyaka kura-kurai da aka samu za su yi tasiri wajen inganta harkokin gudanarwa na hukumar INEC a lokuta na gaba.

Dangane da yadda hukumar INEC za ta ci gaba da cin gashin kanta, kungiyar ACF ta ce dole ne hukumar ta yi watsi da duk wani ra'ayi, suka ko kuma kalubalanta domin ci gaba da gudanar da al'amurran ta bisa ga tanadi na kundin tsarin mulki da ya yi ma ta shimfidar hukuma mai zaman kanta.
No comments:
Write Comments