Tuesday

Home Zaben da aka yi ya cutar da al’umman jihar Kano – Abba Kabir Yusuf
Dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, Abba Kabir Yusuf ya ce jam'iyyarsu ba za ta yarda da sakamakon da hukumar zabe ta bayyana ba.
Abba kabir yusuf

A hira da yayi da shafin BBC Hausa, an kawo Abba na cewa:  “Zabe da aka yi muna Allah wadai dashi, zabe ne na cutar al’umman jihar Kano, asalima kowa ya rigada ya san cewa jam’iyyarmu ta PDP mu muka ci zabe lokacin da aka kada kuri’u na farko inda aka tabbatarwa da al’umma jihar Kano, na Najeriya daman a duniya baki daya cewa mune muke da rinjaye a wannan kada kuri’a da aka yi. 
“Kuma mun samu kaso 25 a kowani kananan hukumomi, mun cika dukkan ka’idoji na hukumar zabe.”

Kan batun sake zaben da aka ce za a yi tun farko, Abba yace: “Idan anyi zabe na Allah da annabi, wanda al’umma suka yarda dashi babu laifi idan anyi, yayinda aka dawo aka ce sai an sake zabe a wasu mazabu a ckin kananan hukumomi 28 na wannan jiha, mu mun dauka cewa hukumar zabe da jami’an tsaro za su yi ayyukansu tsakani da Allah."

INEC ta bayyana Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyya mai mulki ta APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

KUKARANTA KUMA :- Jam'iyyu 42 ne Basu Amince da sakamakon zaben kano ba :


A baya gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa sabanin rade-radin da ake yi, babu wani rikici a jihar, biyo bayan sanar da sakamakon zaben da aka kammala wanda Dr Abdullahi Umar Ganduje yayi nasara.

Da yake jawabi ga manema labarai a yau Talata, 26 ga watan Maris, kwamishinan bayanai na jihar, Malam Muhammad Garba yace jihar na cike da zaman lafiya yayinda mutane ke gudanar da harkokin gabansu.
No comments:
Write Comments