Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nesanta kan shi da kuma jam'iyyar PDP, daga rikicin siyasar da ya faru a jihar Kano.
Sanarwar da ta fito daga bakin wata ta hannun daman shi, Binta Spikin, a ranar Talatar nan da ta gabata, ta bayyana cewa jama'a na ya da jita-jitar ne saboda kawai su ba ta wa Sanata Kwankwaso suna.
KU KARANTA: Zaben da aka yi ya cutar da al’umman jihar Kano – Abba Kabir Yusuf
A karshe ta yi kira ga magoya bayan Sanata Kwankwason akan su zama 'yan kasa na gari, saboda hakan ne zai saka sunansu ba zai ba ci ba.
Sanarwar da ta fito daga bakin wata ta hannun daman shi, Binta Spikin, a ranar Talatar nan da ta gabata, ta bayyana cewa jama'a na ya da jita-jitar ne saboda kawai su ba ta wa Sanata Kwankwaso suna.
"A lokacin da ya ke gwamnan jihar nan, babban burinsa shine ya ga walwala da jin dadin al'ummar jihar Kano, kuma hakanne ya saka shi ya dinga daukar 'ya'yan talakawa yana fita da su kasashen waje domin karatu."
"Saboda haka ina sanar da jama'a Sanata Kwankwaso bai taba kuma ba zai taba tada tarzoma a jihar Kano ba. Idan ba ku manta ba kwanaki kadan kafin a sake zabe ya fitar da sanarwar cewa mutanen jihar Kano su kwantar da hankalinsu su yi zabe ba tare da tashin hankali ba".
KU KARANTA: Zaben da aka yi ya cutar da al’umman jihar Kano – Abba Kabir Yusuf
A karshe ta yi kira ga magoya bayan Sanata Kwankwason akan su zama 'yan kasa na gari, saboda hakan ne zai saka sunansu ba zai ba ci ba.
"Sannan Sanata Kwankwaso zai yi amfani da wannan damar wurin yi wa wadanda suka rasa rayukansu a wannan zabe. Sannan ya yi addu'a ga wadanda suka ji ciwo Allah ya ba su lafiya."
No comments:
Write Comments