Saturday

Home Zaben Gwamnoni : Jahohin Arewa da PDP kan iya samun Nasarar lashewa.
Jigawa: jihar Jigawa ana ganinncewa jam'iyyar APC da ke mulki a jihar ba za ta sha wata wahala ba wajen lashe zaben na gwamna.

Katsina: Yanzu haka dai APC ce ke da iko a jihar, kuma ana sa ran Gwamnan jihar zai sake lashe zaben sa.


Zamfara: Duk da dai da farko an yi ta takadda game da 'yan takarar APC a jihar, amma daga baya APC din ta samu damar shiga zaben kuma har ma ta lashe dukkan zababbun kujerun 'yan majalisar tarayya. Ana ganin APC zata iya sake lashe zaben gwamna

Kebbi: Masu sharhin harkokin kwallo dai na ganin jihar ta Kebbi kusan ba jam'iyyun adawa ma. Don haka APC na da kyakkyawan zaton zata lashe zaben gwamna.

Borno: Duba da irin yawan kuri'un da APC ta samu zaben shugaban kasa a Borno, ana ganin zaben gwamna ma zai iya zuwa hakan.

Yobe: Ita ma dai Yobe ana ganin APC ce zata lashe zaben jihar musamman ma ganin cewa PDP dake zaman babbar jam'iyyar adawar kasar bata taba mulkar jihar ba.

Kwara: Sakamakon da PDP ta samu a zaben shugaban kasa da kuma faduwar zaben da Sanata Bukola Saraki yayi a zaben da ya gabata, ana ganin dai cewa tamkar 'yar manuniya ce akan abun da zai iya faruwa a zaben gwamna.

Neja: Duk da jam'iyyar PDP na da karfi a jihar ta Neja, amma dai ana ganin cewa APC tafi karfi da farin jini a jihar.

No comments:
Write Comments