Friday

Home Rundunar soji tace ba za ta sassautawa masu ta da rikici ba a zaben gwamnoni da na majalisan jihohi
Shugaban hafsan sojojin Najeriya, Tukur Buratai, ya ce rahotannin sirri da aka samu sun nuna cewa ‘yan siyasa na yunkurin tayar da zaune tsaye domin lalata zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun Jihohi da za a gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Maris.


Ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro da manyan jami’ai da Kwamandojin rundunar ta kasa.

Buratai ya yi nuni ga afkuwar wasu tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar a yayinda aka gudanar da zaben shugaban kasa, inda ya ce, jami’an na shi ba za su saurarawa duk wani dan siyasa da ya yi yunkurin tsalma baki a kan yanda zaben ke gudana ba.

Rundunar soji tace ba za ta sassautawa masu ta da rikici ba a zaben gwamnoni da na majalisan jihohi
Wasun su ma suna da shirin yin shigan burtu a cikin wakilan abokanan hamayyan su, su aiwatar da kisan kai, su yi amfani da kafafen yada labarai na yanar gizo domin yin batunci da yada labaran karya domin lalata aiwatar da zaben cikin lumana. Ba za mu taba amincewa su cimma manufar su ba.

A watan Fabrairu, Shugaba Buhari ya bayar da umurni ga hukumomin tsaro da kar su sassautawa duk wanda ya kwaci akwatin zabe. a sa’ilin da abokanan hamayya suka yi suka a kan hakan, rundunar Sojin cewa suka yi za su tabbatar da bin umurnin na shugaban kasa.

No comments:
Write Comments