Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da tabbacin cewar gwamnatinsa zata kawo karshen aiyukan ta'addanci a jihar Zamfara tare da bayyana cewar yin hakan na daga cikin abubuwan da ya bawa fifiko.
Bayan ya sha fama da matsin lamba a kan ya yi magana a kan tabarbarewar tsaro a jihar Zamfara, s
An samu kiraye-kiraye da zanga-zanga daga 'yan Najeriya dake cikin gida da na kasashen ketare a kan a saka dokar ta baci a jihar Zamfara saboda yadda 'yan bindiga ke kashe mutane a kullum.
A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ya fitar, Buhari ya ce zai dauki duk wani mataki da zai bawa jami'an tsaron Najeriya damar murkushe duk wasu makiya Najeriya.
Bayan fitar da wannan sanarwa da Garba Shehu ya yi, shi kansa shugaba Buhari ya bayyana cewar bai amince da zargin da wasu ke yi masa a kan cewar bai damu da asarar rayukan da ake yi a jihar Zamfara ba.
Top3
A jerin wasu sakonni da ya fitar a shafinsa na tuwita, shugaban Buhari ya ce; " abin mamaki ne da rashin adalci a ce ban damu da halin da jihar Zamfara ke ciki ba ko kuma bana yin komai a kai. Babban aiki na a matsayin shugaba shine tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin 'yan Najeriya. Babu wani abu dake raina fiye da yin hakan.
DUBA WANNAN: Kisan kare dangi: 'Yan Zamfara sun gudanar da zanga-zanga a Abuja
"A shirye muke domin ganin mun shawo kan kalubalen tsaro tare da murkushe masu kashe mutane. Mun tura jami'an tsaro zuwa dukkan sassan da ake kai hare-hare, kuma zamu cigaba da sabunta hanyoyi da dabarun yaki da aiyukan 'yan ta'adda.
"Ina tuntubar shugabannin rundunar tsaro domin jin abubuwan dake faruwa a Zamfara da ragowar sassan kasa. Ina bayar da tabbacin cewar zamu cigaba da bawa jami'an tsaro hadin kan da suke bukata domin ganin sun kawar da duk wani kalubalen tsaro da muke fama da shi."
No comments:
Write Comments