Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta ce a kalla shaguna 35 suka kone sakamakon wata gobara da tashi a 'Yan nama da ke cikin kasuwar Kurmi.
Alhaji Saidu Mohammed, kakakin hukumar, ne ya tabbatar da faruwar hakan yayin da yake magana da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yau, Lahadi, a Kano.
Ya ce gobarar ta kone shaguna 27 kurmus, yayin da kone sassan wasu shaguna 8.
DUBA WANNAN: Atiku ba dan Nigeria Ba ne : Apc ta bayyanawa kotu.
Ya bawa 'yan kasuwa shawarar su kasance masu kula sosai da kuma kiyaye wa wajen amfani da duk wasu kayayyaki da kan haddasa tashin wuta domin gudun sake samun afkuwar irin wannan hatsari.
Sannan ya kara da cewa har yanzu ana gudanar da bincike domin gano silar tashin gobarar.
SOURCE : LEGIT. NG

" Da misalin karfe 4:56 na safe wani mutum mai suna Ado Musa ya kira mu tare da sanar da mu cewar gobara ta tashi a kasuwar.
"Nan da nan muka aika jami'anmu da motocin kashe gobara, sun isa wurin da misalin karfe 5:03 domin hana wutar gobarar yaduwa zuwa sauran shaguna," a cewar sa.
DUBA WANNAN: Atiku ba dan Nigeria Ba ne : Apc ta bayyanawa kotu.
Ya bawa 'yan kasuwa shawarar su kasance masu kula sosai da kuma kiyaye wa wajen amfani da duk wasu kayayyaki da kan haddasa tashin wuta domin gudun sake samun afkuwar irin wannan hatsari.
Sannan ya kara da cewa har yanzu ana gudanar da bincike domin gano silar tashin gobarar.
SOURCE : LEGIT. NG
No comments:
Write Comments