A jiya Litinin ne, Shugaban Karamar Hukumar Sanga dake jihar Kaduna, Mista Charles Danladi, ya ankarar da jami’an tsaro a kan wani gaggarunmin shiri da wasu ke yi na haifar da tashin hankali a yankin.
Mista Danladi ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya gabatar a garin Kaduna, inda ya kuma kara da cewa, mutanen sun yi gangami ranar Lahadi inda suka shirya tayar da tarzoma a yankin.
Ya kuma kara da cewa, masu wannan shirin sun shirya watsa labaran karya na cewa, masu neman tayar da fitinan suna son yada cewa, wai mataimakiyar gwamnan na shirin sauke shugaban karamar hukumar saboda wai kirista ne.
KARANTA KUMA : Yan Boko Haram sun bankawa kauyen Chibok wuta
Duk da cewa, Danladi, bai zaiyana sunayen mutanen da ake zargin ba amma ya tabbatar wa da jama’a cewa, karamar hukumar ta yi dukkan abin da ya kamata na ganin ba a sake samun barkewar abin da ya faru a yankin Nandu ba kwanakin baya ba.
Haka kuma shugaban karamar hukumar ya ce, hukuma samar da agajin gaggawa ta jihar SEMA sun samar da kayan tallafi ga al’umma yankin Nandu bayan da aka kai masu harin.
“Karamar hukumar na kokarin gyara gidajen jama’ar da aka lalata kafin zuwa ruwan sama.
“ A kan haka muke kira ga jami’an tsaro su gagauta hukunta dukkan wadanda suke da hannu wajen shirin tayar a hankalin jama’a a fadin karamar hukumar,“ inji Danladi.
Mista Danladi ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya gabatar a garin Kaduna, inda ya kuma kara da cewa, mutanen sun yi gangami ranar Lahadi inda suka shirya tayar da tarzoma a yankin.
“Ina mai sanar da al’umma wani shiri da wasu mutane suke yi na tayar da rikicin addini a yankin karamar hukumar Sanga, ina kuma bukatar ku gaggauta kawo dauki tare da samar da cikkaken tsaro da zaman lafiya a yankin gaba daya.
“Wadanda suke wannna shirin sun yi taro a Kaduna a karkashin wata jam’iyyar siyasa a karshen mako.
“Da yammacin ranar Lahadi 31 ga watan Maris 2019 sun aika kudade karamar hukuma Sanga don ayi amfani da su wajen gudanar da zanga zangan da suka shirya yi ranar Talata 2 ga watan Afrilu 2019.
“Bayanan da muka samu yana nuna cewa, mutane na kokarin haifar da rikicin addinini ne a hanyar kawo raraba a tsakamin mutanen yankin wanda daga nan ne mataimakiyar zababbabiyar gwamna Dakta Hadiza Balarabe ta fito,“ inji Danladi.
Ya kuma kara da cewa, masu wannan shirin sun shirya watsa labaran karya na cewa, masu neman tayar da fitinan suna son yada cewa, wai mataimakiyar gwamnan na shirin sauke shugaban karamar hukumar saboda wai kirista ne.
“Babu wani labari mai kama da haka kuma masu wannan shirin na sane da hakan, amma suna yada karya ne don haifar da tashin hankali a yankin, mutane dake zaman lafiya da juna na tsawon lokaci.
“A matsayi na shugaban karamar hukumar Sanga, hakki nane na tabbatar da an samu cikakken zaman lafiya a yankin, tare da kuma kaucewa barkewar rikici a fadin karamar hukumar dama jihar gaba daya.
“A kan haka ne muke masu zama a cikin shiri don bankado dukkan wani shiri na haifar da tashin hankalin da zai iya cutar da jama’armu ta hanyar yada jita jita da karya a tsakanin al’umma,“ inji shi.
KARANTA KUMA : Yan Boko Haram sun bankawa kauyen Chibok wuta
Duk da cewa, Danladi, bai zaiyana sunayen mutanen da ake zargin ba amma ya tabbatar wa da jama’a cewa, karamar hukumar ta yi dukkan abin da ya kamata na ganin ba a sake samun barkewar abin da ya faru a yankin Nandu ba kwanakin baya ba.
Haka kuma shugaban karamar hukumar ya ce, hukuma samar da agajin gaggawa ta jihar SEMA sun samar da kayan tallafi ga al’umma yankin Nandu bayan da aka kai masu harin.
“Karamar hukumar na kokarin gyara gidajen jama’ar da aka lalata kafin zuwa ruwan sama.
“ A kan haka muke kira ga jami’an tsaro su gagauta hukunta dukkan wadanda suke da hannu wajen shirin tayar a hankalin jama’a a fadin karamar hukumar,“ inji Danladi.
No comments:
Write Comments