Hukumar Raba Hasken Lantarki ta Kasa (NERC), za ta fara tilasta yin amfani da mita daga ranar 1 Ga Mayu.
Jami’in Hulda da Jama’a na NERC, Usman Arabi ne ya bayyana haka, tare da cewa za a fara raba mita ga jama’a a karkashin tsarin MAP, wanda gwamnatin tarayya ta bullo da shi.
Ya ce tsarin raba hasken lantarki ta Sashe na 4(3), ya bukaci kowa ya yi amfani da mita domin a rage matsalar da ake fuskanta.
Arabi y ace masu amfani da wutar lantarki daga Kamfanin AEDC na Abuja da kuma JEDC na Jos, za su iya samun mita bayan kwanaki goma kacal da biyan kudin mitar.
Ya ce kowa har gida za a je a daura masa ta sa.
“MAP za su caji naira 36,991.50 ga wanda zai daura layin wuta daya tilo a gidan sa. Shi kuma wanda zai daura layi biyu, to zai sayi mita mai layi uku a kan kudi naira 67,055.85.
Arabi ya ce mitar ta yi tsada ne saboda an hada “farashin ta har da ladar aikin kaiwa har gida, daurawa, ladar zuwa a gyara maka idan ta lalace, ko kuma a canja maka wata idan ba za ta iya gyaruwa ba.”
No comments:
Write Comments