Wednesday

Home Tirkashi : Yadda el-rufa'i yayi arangama da masu garkuwa da mutane a hanyar Abuja
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i ya yi arangama da masu garkuwa da mutane yayinda suke kokarin sace matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja da ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu, 2019.

El'rufa'i kaduna

Wani jawabin da mai magana da yawun gwamna, Samuel Aruwan, ya saki ya nuna cewa a ranar Laraba, gwamnan ya nufi birnin tarayya Abuja sai ya isa kauyen Akilubu misalin karfe 3:40 na rana, kawai sai ya hagi tarun motoci kan hanya inda sukace masu garkuwa da mutane na kan gaba.

KU KARANTA: A karon farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano.

Yace: "Jami'an tsaron gwamnan sun kawar da masu garkuwa da mutanen wadanda suka arce cikin daji."
"Bayan bude hanyar, gwamna El-Rufa'i ya bada umurnin cewa wadanda yan bindigan suka jiwa rauni a kaisu asibiti da gaggawa."
"Kana gwamnan ya umurci jami'an tsaro su tsananta sintiri a hanyar domin kawar da yan barandan."

Mun kawo muku rahoton cewa sakamakon hare-hare da garkuwa da mutanen da ya addabi babban hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Birnin gwari, majalisar tsaron jihar Kaduna ta yanke shawaran karfafa sintiri a hanyoyin domin rage hare-haren.

Masu garkuwa da mutane sun dawo hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma hanyar birnin gwari. Tsakanin ranar Lahadi da Litinin kadai, an yi garkuwa da akalla mutane 42.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments