Wednesday

Home Tofa!! Dangote ya bayyanawa matasa hanyar da za su zama kamar shi
Hamshakin mai kudin ya bayyanawa matasan hakan a lokacin da ya yi wata hira ta musamman da mashahurin mai kudin nan dan kasar Sudan, Mo Ibrahim a Abidjan, babban birnin kasar Kwaddibuwa, a karshen makon da ya gabata.

hamshaki dangote

Wani wanda ya halarci taron ya yiwa Dangote wasu tambayoyi, inda ya ke tambayar shi wane fanni zai fi mayar da hankali inda ace shi matashi ne dan shekara 21 a duniya, sannan kuma yana da sha'awar fara kasuwanci?

Attajirin ya ce zai fi mayar da hankalin shi akan harkokin sadarwa na zamani da kuma fannin noma.

"Wadannan su ne bangarori biyu da za su fi kowanne bangare kawo riba," in ji Dangote.

Sannan kuma mai kudin ya shawarci matasa akan irin dabi'un da suke da su bayan sun fara kasuwanci, musamman ma matasa na yankin Afirka.

Ya ce, "Matasa su na kashe ribar da ba ta zo hannunsu ba idan suna kasuwanci."

"Daga mutum ya fara kasuwanci kuma ya fuskanci kasuwancin yana samun cigaba, maimakon ya yi ta kara jari, sai kaga mutum ya kashe ribar kasuwar a tunanin shi na cewa ribar za ta cigaba da zuwa," in ji attajirin.

KU KARANTA: Yadda aka kama wasu mutane 3 yayin da suke yunkurin tono gawa daga kabari. 

Dangote ya ce, "Idan mutum ya sayi manyan abubuwa na kyale-kyale da more rayuwa, za su dauke masa hankali daga harkokinsa na kasuwanci."

Mai kudin ya bada misali da kansa, in da ya ke cewa, "a yanzu haka bani da wani gida da nake zuwa domin na shakata, wanda ya ke mallakina a fadin duniyar nan."

"Amma kuma akwai da yawa daga cikin masu yi mini aiki da suke da gidajen shakatawa a birnin Landan." in ji Dangote.

Alhaji Aliko dangote dai shine mutum na daya da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Dangote cikakken Bahaushe ne, wanda ya fito daga jihar Kano da ke yankin arewacin Najeriya. Tun lokacin da ya zama na daya a nahiyar ta Afirka har yanzu ba a samu wani wanda ya ko kama kafarshi ba a nahiyar.

To sai dai kuma ba kasafai aka fiya samun masu kudi suna fitowa fili suna ba wa mutane shawarwari ba musamman masu kudi na nahiyar Afirka.

SOURCE LEGIT. NG
No comments:
Write Comments