Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da wasu mutane uku a gaban alkalin kotun Majistare da ke zamanta a Iyaganku a ranar Talata inda ake zarginsu da yunkurin hakko wata gawa daga kabarin domin su yanke sassan jikin ta.
'Yan sandan suna tuhumar Tayo Badmus mai shekaru 34; Adeleke Ridwan mai shekaru 20 da Saheed Akorede mai shekaru 41 duk mazauna garin Apata da ke Ibadan da aikata laifuka biyu na hadin baki da yunkurin hako gawa.
Jami'in dan sanda mai shigar da kara, ASP Amos Adewale ya shaiwa kotu cewa wadanda ake zargin sun hada baki ne sun aikata laifin a ranar 19 ga watan Maris misalin karfe 1:15 na dare a Alapata da ke Apata a Ibadan.
DUBA WANNAN: Lokacin zafi :Shin ko Ka San Cutar Sankarau?.
'Yan sanda sun gurfanar da mutune 3 da aka kama suna hakko gawa
Adewale ya ce wadanda ake zargin sunyi yunkurin hako wata gawa da ake birne a unguwar da niyyar su yanke sassan jikin ta amma aka kama su.
Ya ce mutanen unguwan ne suka cafke su kuma suka mika su hannun 'yan sanda.
Ya ce laifin ya sabawa sashi na 516 da 508 kuma sashi na 509 da dokar masu aikata laifi na jihar Oyo, 2000 ya tanadar da hukuncin wanda aka samu da irin wannan laifin.
Top3
Sai dai wadanda ake zargin sun ce ba su aikata laifin ba.
Alkalin kotun, Mr Emmanule Idowu ya bayar da belin wadand ake zargin a kan kudu N100,000 kowannen su tare da gabatar da wadanda za su karbi belinsu.
Idowu ya ce dole wadanda za su karbi belinsu su kasance ma'aikatan gwamnati da kuma mutumin da ke da aiki kwakwara.
Ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Yuli kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.
SOURCE LEGIT. NG

No comments:
Write Comments