Wednesday

Home Yadda mutanen Najeriya za su ba Duniya mamaki – Cewar Osinbajo
Rahotanni sun zo mana cewa mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa irin kokarin da mutanen kasar nan su ke yi a fannin fasaha, ya na iya ci da kasar gaba. Farfesa Yemi Osinbajo ya ke cewa irin kwazon ‘Yan Najeriya ya na iya zama sanadiyyar kawowa kasar mafita a kan matsalolin fasaha na zamani da za su sa Najeriya ta rikide a sahun Duniya. 

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi wani zama da wasu kwararru a kan harkokin kasar waje da masu zuba hannun jari a Najeriya a Birnin New York na Amurka. Babban hadimin mataimakin shugaban kasar watau Laolu Akande ya ke cewa, Osinbajo ya bayyana wannan ne a lokacin da a ka jefe sa da wasu tambayoyi kan rikicin fasahar Duniya.

Osinbajo ya ce: “Ba mu son wani rikici a halin yanzu. Mu na maraba da duk wani kamfani da zai zo kasuwanci Najeriya. Huawei su na Najeriya yanzu haka tare da wasu manyan kamfanoni.” 

KU KARANTA: Gwamnan Yobe zai aika ‘Dalibai zuwa karatu a kasar waje

 “Ba mu kai ga yanke shawara a game da sha’anin fasahar 5G ba. Idan a na maganar fasaha, sai mu tambaya ta ya kasar Sin su ka kai ga haka? Ta ya sauran jama’a su ka yi nisa? Mu ma za mu kai ga haka da kan mu.” 

Mataimakin shugaban kasar ya cigaba da cewa gwamnatin Najeriya za ta yi amfani da baiwar da Ubangiji ya yi wa Matasan Najeriya wajen cin ma burin kasar.

Wannan zai sa kasar ta yi zarra a ban kasa. “Mu na da kasuwar wayar salula na sama da mutane miliyan 174 a Duniya. Najeriya na cikin manyan kasuwannin salula 10 a ban kasa.” Inji Osinbajo.

 Ya cigaba da cewa: “A Duniya, mu ne na 2 a Duniya wajen kasuwanci ta yanar guzo, bugu-da-kari akwai ‘yan Najeriya miliyan 17 da ke amfani da Facebook.
“Kamfanin Microsoft sun yi alkawarin kafa cibiya ta Dala miliyan 100 a Najeriya domin Nahiyar Afrika.” kamar yadda Laolu Akande ya bayyana a jawabin na sa.

SOURCE LEGIT.NG 
No comments:
Write Comments