Showing posts with label dandalin waya. Show all posts
Showing posts with label dandalin waya. Show all posts

Friday

Yadda zaku maida lambar wayar ku zuwa ta kasashen waje. in 5min - Android tricks.

Assalama Alaikum ma'abota wannan shafi kamar Kullum wannan shafi namu yana tafe muku da wata Hanya zai iya kasan cewa wasu Sun Sani Amma wa’inda Basu Sani ba sunfi wa’inda Suka Sani Yawa
Ita dai wannan hanya ce da zata baka damar mayar da LAMBAR WAYARKA KA
ZUWA NA WATA KASAR DABAN.

Da farko dai za kuje site dinnan wanda Zan baku link din ga Adreshin SITE din kamar haka.
http://www.uknumber.co.uk/

Da zarar kun shiga site din za kuga wajen zabar Country kamar haka. 
Yadda ake,  Yadda ake chanza, Yadda ake canza lambar waya zuwa wata kasa,  how to change phone number to another country
To anan ne zaku zabi kasar da kuke wato ida a nigeria kake sai ka zabi nigeria , in kuma aa nijar kake sai ka zabi nijar  ku mayar.

Za muyi misali da nigeria, bayan kun zabi kasar da kuke to zaku ga sun bada wajen saka lamba, to sai ku saka lambar ku, ina nufin lambar da ku keso idan ankirawo lambar UK zata shigo a lambar da kake amfani da ita a nigeria.

 Wajen da suka bada na saka lambar zakuga akwai country code na nigeria wato 234 to kwai sai ku karasa da lambar taku, Amma kar ku saka 0 ta farkon lambar, misali lambarka itace 09037621927 to idan kazo sai ka saka 9037621927 kaga zai zama 2349037621927 kenen.

Bayan ka saka lambar ka kamar yadda mukayi  bayani kawai sai ka danna submit button , zaka ganshi a gefen inda ka rubuta lambarka an rubuta "Click to get your number" , To sai ka danna shi.

Bayan  ka danna button din , a page na gaba da zai bude zasu  baka form da zaka cike, kamar haka.

Yadda ake,  Yadda ake chanza, Yadda ake canza lambar waya zuwa wata kasa,  how to change phone number to another country
A wannan form ne zaka saka suna, adireshinka, Email da sauransu, Ka tabbatar ka sak email dinka dai-dai don tanan zasu turo maka pin da zaka tabbatar da lambarka (Verify).

Da zarar ka cike komai dai-dai sai ka danna submit button, zaka ga sun cemaka CONGRATULATIONS.
Yadda ake,  Yadda ake chanza, Yadda ake canza lambar waya zuwa wata kasa,  how to change phone number to another country

Bayan kaga wannan , sai ka duba inbox na email naka sun tura maka da pin. kamar haka.

Yadda ake,  Yadda ake chanza, Yadda ake canza lambar waya zuwa wata kasa,  how to change phone number to another country

Bayan duk ka kammala wadannan matakan, yanzu sauran mataki na karshe , shine Verify.
karka  manta lambar bazata fara aiki ba sai kayi activate (VERIFY)

YADDA ZAKAYI VERYFY NA SABUWAR LAMBAR KA.

Bayan ka samu pin naka a email sai ka duba kasa kadan zakaga rubutu suna bayanin yadda zakayi verify na lambar, To yadda zakayi shine.

Akwai lambar da suke badawa a kirawo ta don yin verify , lambar itace +442070439799 , zaka ganta a rubutun da yake kasan pin naka.

Sai ka kira wannan lamabar zakaji sun yi maka welcome, zasu ce ka saka lambar wayar, suna nufin sabuwar lambar da suka baka ta email wadda take a saman pin naka. Sai ka sakata, bayan ka gama sawa zasuce ka saka pin, sai kayi sauri ka saka pin wanda suka aiko maka ta email. bayan ka saka pin zakaji sunce maka, YOUR NUMBER IS NOW ACTIVATED, wato ka gama komai kenan.

Daga nan sai ka jira akalla awa 10hours ko 8hours, kafin ka gwada aiki da ita, idan zaka kira lambar dolene kasa country code na UK wato 44, misali sun wannan lambar suka baka 08012345678, to idan ka tashi kira sai ka cire 0 na farko ka saka 44 , wato zata zama haka kenan 448012345678.

Kar ka gwada kiran da lambarka wacce kayi register da su, zai zaman kamar kana kiran kanka da kankane.

ka gama komai kenan , yanzu zaka iya amfani  da lambobi  kala biyu a layin waya daya, sannan wannan sabuwar lambar  da ka samu bazata shafi tsohuwar lambarka ba, zaka  iya karbar kira daga kowacce a cikinsu, a kowanne lokaci. kudin kiran 50kobo ne per 1second.

Sannan idan kanaso lambar ta zauna akalla duk bayanan wata 1 ko 2 zaka dinga renewing na wannan lamabar wato sabuntawa.

IMPORTANAT NOTE ; Wajen kiransu don yin activating karka gwada da MTN , ka nemi layin GLO, AIRTEL ko 9MOBILE , don Layin Mtn bayayi.

NEMAN KARIN BAYANI? WHATSAPP ME @ +2349037621927

Thursday

Yadda Ake Chatting Da Bluetooth ba tare da Data Connection ba : Android tutorial

Bluetooth chat Android Tutorial.
- Android tricks 2020
- Android tutorial 2020
- Best android appS 2020

BARKAN MU DA WANNAN LOKACI DA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA.
-
-
Bluetooth Chat ba sabon application bane. An ɗan jima ana amfani da shi, yanzu haka yana nan a playstore inda mutane sama da dubu ɗari suke amfani da shi, sunan wanda ya assasa wannan application Glodanif.
Bluetooth chat Android tutorial
Bluetooth chat Android tutorial

Wannan Application me suna Bluetooth Chat zai temaka maka wajen aika taƙaitattun saƙonni da hotuna, zaka iya chatting da abokanka ta wannan application matsawar bluetooth naku zayi connect, to zaku iya amfani dashi ba tare da internet connection ba.

Musamman ɗalibai zai matuƙar taimaka muku a yayin da babu Wi-fi a makarantarku, matafiya ma wannan application zai taimaka ƙwarai yayin da suke cikin tafiya yayin da suke cikin tsaunuka, koda babu network a wannan waje zasu iya amafani da wannan application wajen isar da saƙonni zuwa ga juna.

Da akwai abubuwa da yawan gaske wanda wannan application yake taimakawa kawai don isar da saƙonni yayin da babu Network a waje.
Idan abokin ka ko ƙawarki bata da wannan application, kuma babu internet connection da zai bada damar sauke wannan app to abune mai sauki zaku iya sharing na app din ta hanyar bluetooth ba tare da wata wahala ba. ku duba matakan da ake bi a saita wannan app a kowacce irin android.

Yadda Ake Amafini da Bluetooth Chat ba tare da Data connection Ba.⤵⤵

YADDA AKE SAITA BLUETOOTH CHAT APP.

1 - Babu shakka ana buƙatar data don sauke wannan  App zuwa kan waya don yin installing. Girman application ɗin 2.4MB ne kawai , akwaishi a playstore , ko kuna kuyi download kai tsaye ta nan Download Here.

2- Bayan kunyi download sai kuyi install, bayan ya gama installing sai ku buɗe app ɗin, da zarar kun buɗe zakuga wajen saka suna, zaɓar colour, idan kuka cike abin da ake buƙata kawai sai ku danna save.
Yadda Ake Chatting Da Bluetooth ba tare da Data Conection ba  Android tutorial, Bluetooth chat Android tutorial

3 - Ku tabbatar ɗaya wayar da kuke son yin connecting da ita , bluetooth nata a kunne yake. Sai ku danna Scan.

4 - Bayan kun danna Scan sai ku duba ɗaya wayar zakuga pairing request ya bayyana akan screen na wayar, sai ku danna "Pair", da zarar kun danna, duka wayoyin biyu zasuyi connected.

5 - To yanzu komai ya zama ready zaku iya fara aika sakonni da hotuna, kai har ma da emojis.


DUBA WANNAN KUMA.

- Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki

- Yadda zaku maida lambar wayar ku zuwa ta kasashen waje. in 5min

- Yadda Zaku Bude Facebook Account Ba Tare Da Suna Ba.


Open Facebook Account With Invisible Name, Yadda Zaku Bude Fb Account Ba Tare Da Suna Ba.

Barka da warhaka da fatan kuna cikin koshin lafiya.

Yau muna tafe da bayani akan yadda zaku bude FACEBOOK ba tare da suna a jiki ba.

Step 1) Da farko ku bude wannan link http://facebook.com a wayoyinku na android, sannan ku danna Create New Account.


Step 2) Sai ku canja yaren English  Zuwa Yaren Tamil language. Kamar yadda kuke gani a hoton kasa

To Yanzu sai ka nutsu da kyau,, Sannan kabi wadannan steps a nitse , da kuma screen shots  da zaka gani.


1) invisible name fb account text code : wato sunan da zakayi amfani dashi a wajen first name.

 ---->ゖゖ 💟@() ゖ ✔<----

Yanzu kayi copy na wannan code dake sama wanda yake tsakani Arrows (between arrows-->__<--) Sai kayi paste a wajen first name.

2) Yanzu sai ka saka lambar wayarka a email box. Kayi amfani da lambar da ba'a taba bude fb account da ita ba. Sannan kar kayi amfani da email, lambar wayarka kawai zaka saka a email box.

3) kayi selecting na Gender.


4) ka cike date of birth.


5) ka cike wajen Password { ka zabi secure password. Wanda yake da capital latter, Lambobi hade da special word kamar su @ $ # : ! ?.}

Step 3) Bayan ka gama ciccikewa sai ka danna Sign Up. Duba wannan screen shot ! 

Bayan ka dannan singup Zasu turoma da Confirmation Code zuwa lamar da ka saka . Sai kayi amfani da code din kayi comfirm na account naka.


BAYAN DUK KAGAMA WANNAN SAI KA MAIDA YAREN YA KOMA ENGLISH.

Ga yadda zakaga sabon account naka wanda ba suna.


Shikenan yanzu ka bude facebook account wanda ba suna a jiki.

Ku cigaba da kasancewa da wannan shafi mai albarka.

Tuesday

Yadda Ake Connecting Na Android Xender Da Computer. : Android Tutorial 2020


Assalamu'alaikum Barkan mu da yau, Da fatan kowa lafiya.


 Ayau muna ɗauke da cikakken bayani aka Yadda ake connecting na xender ta wayar android zuwa computer ta hanyar wifi, wannan hanya tanada mauƙar sauri wajen tura files zuwa kan computer ko kuma turawa daga computer zuwa kan waya, a wannan zamani cigaba yazo matuƙa sakamakon idan kukayi duba zuwa shekarun suka gabata ana amfani da bluetooth ne wajen transper na files daga wannan wayar zuwa wannan wayar, a yanzu kuma cigaba yazo ida ake amfani da Xender wadda tafi bluetooth sauri nesa ba kusa ba, idan kuka biyo wannan rubutu namu a yanzu zaku laƙanci yadda ake connecting na android xender da kowacce irin computer, wannan yana aiki akan kowacce waya matuƙar dai android ce.

Aika files ta amfani da wannan hanyar yana da matuƙar sauki da kuma saurin aiki.

Mene yasa zanyi amafani da wannan hayar don kawai tura files zuwa computer?

- Yana iya kasancewa USB naka ya lalace.

- Wayarka ta android bata iya connecting da computer.

- Kana son Tura Large files kamar Bidiyoyi ko kuma Games masu Nauyi.

- Ko kuma dai kawai kanason gawadawa don Gaba.

Abubuwan da ake buƙata sune :


  • - Wayar Android , Application na Xender a cikin wayarku ta Android
  • - Computer , Chrome, firefox ko opera ko kuma duk wata browser mai ƙarfi a cikin coputer ku.

Step 1.
Ku buɗe xender Application na cikin wayarku ta Android, sai ku taɓa icon na option wanda yake a sama daga ɓangaren hagu, (duba hoton ƙasa).

Step 2.
Bayan kun taɓa wannan icon na option, Da zarar ya buɗe zakuga inda aka saka Connect to PC, kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa.

Step 3.
Bayan kun taɓa Connect to PC , waje na gaba zai buɗe , anan zakuga option guda biyu, akwai WEB CONNECT akwai HOT SPOT, to ku Zabi Hot spot kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa, sai ku taɓa CREATE HOT SPOT , zaku ganshi daga kasa. (duba hoton kasa)

Step 4.
Bayan kun taɓa create hot spot, zai fara loading bazai ɗauki lokaci ba , cikin ƴan sakanni zai nuno muku wasu Lambobi, kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa.

Sai ku kwafi Wannan lambobin ku rubutasu dai-dai a address bar na browser ta computer ku, kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa.


Da zaran kun gama rubutasu dai-dai kamar yadda kuka gansu to sai ku danna enter , wato a computer kenan.

Kuna dannawa zai fara loading , cikin ƴan sakanni zakuga wayar ku ta android tayi motsi (ba motsin jiki ba), To sai ku taba Accept, kamar haka⤵⤵⤵

Shikenan A yanzu kunyi connect na Android da Computer ta hanyar Amfani da Xender Application, Yanzu mun gama bayani akan yadda ake connect ,sai bayani akan Yadda Zaku tura files tsakanin computer zuwa waya ko daga wayarku zuwa computer, sai ku biyo mu.

YADDA AKE TURA FILES DAGA COMPUTER ZUWA A WAYA TA HANYAR AMFANI DA XENDER.


Bayan kun gama da gabaɗaya waɗancan matakan na sama wato yadda ake connect, bayan komai yayi connected to a lura, za'ayi amfani da computer ne wajen aikin walau tura files zuwa waya ne ne ko kuma tura files daga waya zuwa computer ne , to duka da computer zaku yi, waya kuwa sai dai ku ajiyeta a gefe kuma.

Ku biyo waɗannan matakan don sanin yadda ake turawa.⤵⤵⤵

Step 1.

Bayan komai yayi connected, idan kuka duba screenshoot na ƙasa zakuga inda aka sa UPLOAD MUSIC , to wannan button na upload shine zai baku damar aikawa da files zuwa wayarku ta Android wadda ku ka ajiye a gefe.

Step 2.

A wannan hoton na ƙasa kuma zakuga inda aka saka alamar DOWNLOAD, wato daga gefen Upload Button, to wannan Download button shine zai baku damar turo files daga wayarku dake ajiye a gefe zuwa computer.

Wanna shine cikakken bayani akan yadda ake connecting na Android Xender da Computer don Tura files.

DUBA WANNAN KUMA.

Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki

Yadda zaku maida lambar wayar ku zuwa ta kasashen waje. in 5min

Yadda Zaku Bude Facebook Account Ba Tare Da Suna Ba.

Yanda Zaka Samu Rancen Kudi Har N100,000 A Layin Etisalat New(9mobile)  

Yadda Ake Connecting Na Android Xender Da Computer. : Android Tutorial 2020. 

Ko kuma Ku ziyarci Page namu mai tâken YADDA AKE....🔗🔗



Friday

Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki

Me Yasa Whatsapp suke dakatar da Lambarka daga Amfani da Manhajara su ta Whatsapp.?


Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki


Whatsapp wani fitaccen Application Ne da yake bawa mutane da mar Aika saƙonni nan take, Miliyoyin Jama'a ne suke Amfani da shi a kulli-yaumin, ana iya amfani da shi ta hanyoyi da yawa kamar, aika saƙo na rubutu , na video, na audio ko na hoto, kai harma ana iya yin kira kai tsaye da manhajar ta whatsapp.

Idan ya kasance kana karya dokoki da ka'idojin whatsapp ko kana in wasu halaye da basu kamata ba to ba shakka zasu iya kulle maka account na dan wani lokaci.

Akwai Dalilan da yasa ake dakatar da mutum daga amfani da whasapp, wanda idan har kuka karya su to kuna iya samun matsala da whatsapp, kuskuren farko da mutane sukeyi shine basa karanta sharuddan kafin su bude account na whatsapp, Na kawo wasu manyan dalilai da zai sa whatsapp suyi banning na lambarku ba tare da bata lokaci ba.

Daga cikin dalilan Akwai:-
  • Sending bulk messages to unlisted contacts
  • Sharing website URLs and ad links for multiple times a day
  • Creating porn & adult-related groups and broadcasts
  • Blocking your WhatsApp number by many people
  • By uploading content status which is abusive or it may contain adult things.
Wani lokaci , wasu daga cikin dalilan sukan sanya whatsapp suni banning na account na dan wani lokaci, kamar na tsawon awa-72 ko kwana uku, "Whatsapp sunyi banning na lambata har tsawon awa72 daga baya kuma ta dawo aiki".

Domin ka kaucewa irin wannan dakatarwa da whatsapp sukeyi , ya zama lallai kabi dokokin su, ba tare da karya ka'idojin da suka gindaya b, idon karya wasu kananan dokoki, to whatsapp zasu iya kulle maka account a matsayin gargadi, sannan kuma za'a dawo maka da account din bayan kammala kwanakin da suka tsara.

Yadda za a tsere daga WhatsApp Bannig na har abada.

(Wato permanent Ban)

Ko kana aikata irin wancan kuskuren wanda aka zayyano a sama? to karka damu a yanzu haka zaka samu mafita.

Matakan da zakabi wajen dawo da lambarka da aka dakatar daga yin whatsapp.
  • Uninstall your existing WhatsApp now
  • Download and install new update Whatsapp
  • Enter your phone number and you will see a screenshot like this
Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki

  • - Click on the “Support” option
  • - Now a contact support form is displayed like this
  • - Write your problem and add the screenshot of what it is showing
  • - Don’t forget to add your number
  • - Click “Next” and scroll down
  • - Choose “This does not answer my problem”
  • - Now send a support email using support@whatsapp.com
  • - After 4hrs, check your email inbox. You will get a WhatsApp reply.
Ina tabbatar maka ida kabi wannan matakan na sama to lambar ka zata dawo yin aiki a whatsapp.

NOTE ; Idan kuka gwada wannan steps bai yi ba to ku samu wata lambar ku bude sabon whatsapp. abin da ba'a gane ba contact me here, WhatsApp only +2349037621927.

Yanda Zaka Samu Rancen Kudi Har N100,000 A Layin Etisalat New(9mobile)


Katafaren kamfanin sadarwar nan na Etisalat da yanzu aka canzawa suna zuwa 9mobile sun fito da wani tsari da zai baiwa kwastomomin sa damar cin gajiyar wani tsari da zai rinka basu damar rantar kudi har Naira dubu dari (~N~100,000) zuwa abinda yayo kasa zuwa akawunt dinsu na banki don yin hidindimunsu na rayuwa dasu wanda zasu biya a can gaba.

Yanda Zaka Samu Rancen Kudi Har N100,000 A Layin Etisalat New(9mobile)




Idan baku manta ba ma kamfanin MTN tare da hadin gwuiwar Diamond bank suna da wannan tsari ta hanyar Diamon Y’hello account dake baiwa kwastomomin su damar karbar rancen kudi wanda daga bisani mutum kan biya.

To suma kamfanin na 9mobile sun yunkoro da wani tsari mai suna KwikCash dake baiwa mutane damar karbar rancen kudin.
Ba tare da dogon surutu ba bari nayi muku bayani kan yadda zaku samu wannan rance.

Daga : umar Alkalin fzbuk

Da farko dai sai mutum ya sami Layin Etisalat sannan sai yabi wadannan matakai:
  • – Da farko sai ku danna *561#
  • – Sai a zabi “Request loan”
  • – Wajen preferred loan offer sai a zabi Bank sannan sai mutum ya sanya lamabar akawunt dinshi ta banki(account number)
  • – Daga nan sai ka zabi gabi da tabbatar da yawan kudin da kake son ka ranta din, sannan sai ka karbi “terms and conditions” nasu sannan sai kayi submit..
Idan kana so ka biya bashi to sai ka danna *561#,sai ka shiga wajen Pay loan , sai kabi ragowar matakan sa zasu biyo baya.


Ku sani cewar: kowa na da damar cin moriyar wannan tsari, ma damar mutum na da layin Etisalat(9mobile) sabo ko tsoho..