Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria EFCC, ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema a gaban wata babbar kotun jiha bisa zarge-zargen cin hanci da rashawa.
Ana dai zargin tsohon gwamnan ne da wasu mutane uku da karkatar da Naira biliyan 11 na kananan hukumomi a lokacin mulkinsa daga shekarar 2007 zuwa 2015.
A zaman kotun da aka yi yau Talata a birnin Katsina, lauyoyin tsohon gwamnan sun ce kotun ba ta da hurumin sauraron karar, yayin da su kuma lauyoyin EFCC suka kalubalanci lauyoyin masu kare wanda ake tuhuma.
Babbar kotun dai mai lamba 3 ta sanya ranar 7 ga watan gobe domin bangarorin biyu su tafka mahawara kan batun hurumin kotun.
Bayan zaman kotun dai Ibrahim Shema ya tafi tare da sauran mutane uku da ake tuhumarsu, wadanda da ma suka karkashin belin hukumar EFCC.
A watan Satumbar bara ne tsohon gwamnan ya kai kansa hukumar ta EFCC, kwana daya bayan hukumar ta yi shelar cewa tana neman sa ruwa a jallo.
No comments:
Write Comments