An gudanar da Jana'izar uwargidan marigayi Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu a yau Litinin - Hajiya Shatu ta rasu a jiya Lahadi, 21 ga watan Mayu bayan tayi fama da doguwar jinya a birnin KanoAn gudanar da Jana'izar uwargidan marigayi Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu a yau Litinin, 22 ga watan Mayu. Hajiya Shatu ta rasu a jiya Lahadi, 21 ga watan Mayu bayan tayi fama da doguwar jinya a birnin Kano. Marigayiya hajiya Shatu
Marigayiyar ta rasu tana da shekaru 89 a duniya, ta kuma rasu ta bar jikoki goma sha biyar a duniya. Marigayiya Hajiya Shatu Aminu Kano Ta rasu bayan shekaru 34 da rasuwar mijinta Malam Aminu Kano shahararen dan siyasa a arewacin Najeriya wanda ya kafa jam’iyyar NEPU ta masu ra’ayin rikau na yan mazan jiya.
Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Nigeria Ya Bayyana ta A matsayin Mace Hazika.






No comments:
Write Comments