Shin ko me yasa a kasar Indiya, kusan duk yaron da ya shiga asibitin Baba Raghav na jihar Uttar Pradesh, da gawarsa ake fitowa ?
Shin ko me yasa a kasar Indiya, kusan duk yaron da ya shiga asibitin Baba Raghav na jihar Uttar Pradesh, da gawarsa ake fitowa ?
Ayar tambayar kenan da al'umar ciki da wajen kasar Indiya suka dasa, wanda kawo yanzu ake ci gaba da cece-kuce a kanta.
A 'yan kwanaki 3 da suka shige akalla yara kanana 35 ne suka rasa rayukansu a cikin kwanaki 3 kacal.
Duk da iyalan da suka rasa 'ya yansu na ikrarin cewa, karancin iskar oksijen ne sanadiyar mutuwar 'yayansu,ama kuma Rajiv Rautela wanda wani babban likita ne a asibitin Baba Raghav ya ce wadannan kalaman basu da tushe, domin wa'adin yaran ne ya rige ya cika, shi yasa ba su rayu ba.
Tuni magajin garin Uttar Pradesh ya bada umarnin fara bincike a kan wannan lamarin mai rikitarwa.
Shugbana babbar cibiyar kiwon lafiya ta Pradesh, Praşant Trivedi ya ce ko shakka babu bututan iskar oksijen na matukar matsala amma kuma ba su ba ne umma'aba'isar mutuwar wadannan yaran ba.Domin da yawa daga cikin su, daman basu faye samun lafiyayyen abinci ba,ko kuma sinadirai masu gina halitta.
Daga karshe Rajiv ya sanar da cewa, kamfanin saraffa iskar oksijen na bin asibitinsu dalar Amurka dubu 106 wadanda kawo yanzu sun kasa biyan su.
No comments:
Write Comments