A karon farko Shugaban Majalisar Dattawa, Bokula Saraki ya fito fili ya yi ikirarin cewa Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu mutum ne mai akida a kan abin da ya shafi aikinsa na yaki da rashawa.
Saraki ya ce a zamanin mulkin Jonathan an tura su wajen Magu bisa adawar da suka nuna kan wani kudiri na gwamnati inda aka nemi Shugaban hukumar kan ya bincike su kan wani laifi da ake zargin sun aikata amma da isarsu ofishin Magu, sai ya tabbatar masu da cewa shi ba zai bari a yi amfani da shi wajen biyan bukatar siyasa ba.
A cewar Shugaban majalisar Dattawan, majalisa ba ta da laifi kan kin tantance Magu inda ya nuna cewa matsalar ta taso ne daga rahoton da hukumar tsaro na farin kaya ta gabatar a kansa na cewa bai cancanci rike wannan mukamin ba.
No comments:
Write Comments