An gana ciken daren jiya tsakanin mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da wakilan gamayyar kungiyar kare muradun ‘yan yankin Niger Delta, wadanda a cikin watan nuwambar bara suka bukaci gwamnati ta biya wa ‘yan asalin yankin wasu bukatu 16 ko kuma su janye gudunmuwar da suka bayar domin samar da tsaro a yankin mai arzikin mai.
Wasu daga cikin mahalarta wannan taro sun hada da ministan raya yankin Niger Delta, da kuma wasu tsoffin gwamnoni da ake kallo a matsayin dattawan yankin.
Gwamnatin Najeriya na kokarin kawo karshen rikicin yankin da yanzu haka ta janyo asarar rayukan jama’a.
No comments:
Write Comments